An Gurfanar Da Wani Magidanci Mai Auren Mata 5 A Kotun Musulunci, Alkali Ya Zartar Masa Hukunci

An Gurfanar Da Wani Magidanci Mai Auren Mata 5 A Kotun Musulunci, Alkali Ya Zartar Masa Hukunci

  • An gurfanar da wani ɗan kasuwa gaban wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
  • Ana zargin magidancin da auren mata biyar wanda hakan ya saɓawa koyarwar addinin musulunci
  • Matar da aka auro matsayin ta biyar ɗin ta gaya wa kotu cewa ba ta da masaniya cewa akwai auren ta huɗu akan sa

Jihar Kaduna - Wani magidanci mai suna Awaisu Jibril, ya gurfana a gaban kotun shari'ar musulunci mai zaman ta a Rigasa, Kaduna bisa zargin auren mata biyar.

Mai shigar da ƙara, Insfeta Sambo Maigari, ya gaya wa kotun cewa wani mai unguwa, Musa Abdullahi, shine ya kai ƙorafi kan lamarin ofishin ƴan sanda na Rigasa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

An gurfanar da magidanci bisa zargin auren mata 5
Hatimin kotu Hoto: Ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Wanda ake ƙarar ya bayyana wa kotun cewa matan sa guda hudu ne domin ya saki ta huɗun kafin ya auro ta biyar ɗin.

Kara karanta wannan

Daga Tsana Zuwa Soyayya: Magidanci A Social Midiya Ya Bayyana Yadda Budurwar Da Ta Tsane Shi Ta Zama Matarsa

Sai dai, ya bayyana cewa matar sa ta huɗun bata kammala Iddah ba, domin yakamata ta yi jini uku ne, cewar rahoton Ripples Nigeria

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A na ta ɓangaren, amaryar da aka auro ta biyar ɗin ta gaya wa kotun cewa bata san cewa akwai auren ta huɗun akan sa ba, inda ta ƙara da cewa tana ɗauke da juna biyu na wata ɗaya.

Alƙalin kotun, Malam Anas Khalifa, ya ce kuskure ne ya ƙara auren wata matar bayan ya san cewa matar sa ta huɗu ba ta kammala Iddah ba.

Yayi hukuncin cewa auren sa na biyar ɗin bai halasta ba saboda musulunci bai yarda da auren mata fiye da huɗu ba, inda ya ƙara da cewa junan biyun da matar sa ta biyar ɗin take ɗauke da shi halastacce ne.

"Bayan ƙwaƙƙwaran bincike da samun hujjoji daga wajen shaidu, kotu ta fahinmci cewa wanda ake ƙara ya jahilci hukuncin addinin musulunci kan aure da saki." A cewarsa

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Azumi Wani Abin Fashe Wa Ya Tashi a Wani Babban Birnin Jihar Arewa

"Saboda haka, zai cigaba da ɗaukar dawainiyar Naja’atu Kabir da juna biyun ta har sai ta haihu, zai kuma ɗauki ɗawainiyar abinda za ta haifa bayan an haife shi saboda cikin na sa ne."
“Abinda za a haifa ɗin zai gaji mahaifin sa saboda ba ta hanyar banza aka samu cikin sa ba amma sai a dalilin jahilci da rashin bincike na iyayen sa."

Alƙalin ya kuma tabbatar da saki ɗayan da aka yi wa matar ɗan kasuwan ta huɗu.

Ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 19 ga watan Afirilun 2023, domin yanke hukunci kan wanda ake ƙara.

Kyakkyawar Fahimtar Addinin Musulunci Shi Ne Mabudin Zaman Lafiya Ga Duniya, Buhari

A wani rahoton na daban, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana muhimmancin yi wa karantarwar addinin musulunci kyakkyawar fahimta.

Shugaba Buhari ya ce yi wa addinin musulunci kyakkyawar fahimta shine mabuɗin zaman lafiya ga duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng