Janye Yajin Aiki: Muhimman Yarjejeniyoyi 7 Da Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Da Kungiyoyin Kwadago

Janye Yajin Aiki: Muhimman Yarjejeniyoyi 7 Da Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Da Kungiyoyin Kwadago

  • A daren ranar Litinin ne kungiyoyin ƙwadago na Najeriya, NLC da TUC suka dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni
  • Matakin dai ya biyo bayan taron da wakilan Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin kwadagon suka yi a fadar shugaban ƙasa, kan batun cire tallafin man fetur
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa gwamnati ta ƙulla yarjeniyoyi da NLC da TUC kan batutuwan da suka biyo bayan cire tallafin

Abuja - A ranar Litinin, 5 ga watan Yuni ne ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta ƙulla wasu muhimman yarjejeniyoyi guda bakwai da Gwamnatin Tarayya kafin dakatar da yajin aikin da ta shirya tsunduma a ranar Laraba 7 ga watan Yuni.

ICIR ta ruwaito cewa, ƙungiyar ta shirya shiga babban yajin aikinta na farko tun bayan shekaru takwas baya, sa’o’i kaɗan kafin janyewarta bayan cimma yarjejeniya da gwamnati.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

NLC, TUC da Gwamnatin Tarayya sun cimma yarjejeniya
Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyoyi da kungiyoyin kwadago: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Muhimman yarjejeniyoyi bakwai da Gwamnatin Tarayya ta cimmawa da ƙungiyoyin ƙwadago

Wakilan gwamnati ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne suka ganawa da ƙungiyar NLC ƙarƙashin jagorancin Joe Ajaero da kuma TUC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bangarorin sun cimma matsayoyi, waɗanda suka kai ga dakatar da yajin aikin da suka shirya yi a daren ranar Litinin, yarjejeniyoyin da aka cimmawa su ne:

Duba batun ƙarin albashi

Gwamnatin tarayya da TUC da NLC sun kafa kwamitin haɗin gwiwa don duba ƙudirin ƙarin albashi tare da samar da tsari da lokacin aiwatarwa.

Duba batun tallafin bankin duniya

Gwamnatin tarayya da TUC da kuma NLC za su sake duba tsarin ba da kuɗaɗe na bankin duniya, tare da ba da shawarar shigar da masu ƙananan albashi a cikin shirin.

Batun tsarin CGN

Gwamnatin Tarayya, TUC da NLC za su sa ido kan aikin farfado da shirin sauya tsarin ababen hawa, zuwa masu amfani da iskar gas wanda hukumomin ƙwadagon suka amince da shi a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Kasashen Afirka 10 Da Suka Fi Najeriya Biyan Mafi Karancin Albashi, Har Da Masu 200k

Haɓaka ɓangaren ilimi

Shugabannin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya sun haɗu don duba abubuwan da ke kawo cikas ga samar da ingantaccen ilimi tare da ba da shawarar hanyoyin gyarawa.

Batun matatun man fetur a ƙasa

Hukumomin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya sun haɗu domin duba yadda za a kammala aikin gyaran matatun man ƙasar nan.

Maganar tituna da faɗaɗa layin dogo

Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin kula da tituna da kuma fadada titunan jiragen ƙasa a duk faɗin ƙasar nan.

Buƙatun da ƙungiyoyin suka miƙawa gwamnati

Duk wasu buƙatu da TUC ta mika wa Gwamnatin Tarayya, kwamitin hadin gwiwar zai tantancesu.

Bangarorin kuma sun kuma ƙulla ƙarin yarjejeniyoyi a kan:

  • Kungiyar NLC za ta dakatar da batun yajin aikin nan take domin samun damar tuntubar juna.
  • Kungiyar TUC da NLC za su ci gaba da tuntubar Gwamnatin Tarayya dangane da waɗancan kudurorin da aka zayyano a sama.

A yanzu haka dai, ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya sun amince su sake haɗuwa a ranar 19 ga Yuni, 2023, don yanke shawara kan tsarukan da aka bijiro da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tinubu Ta Shiga Sabon Zama da Kungiyoyin NLC da TUC, Bayanai Sun Fito

Ƙasashe 10 da suka fi Najeriya biyan albashi mai tsoka

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, mun kawo muku wasu ƙasashen Afrika guda 10 da suka fi Najeriya biyan ma'aikatansu albashi mai tsoka.

Ma'aikatan Najeriya dai na ta kokawa kan yadda albashinsu ke gaza biyan buƙatunsu na yau da kullum, musamman ma yanzu da aka cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel