“Ki Barni Na Sarara a Aurena”: Matashiya Ta Roki Budurwar Mijinta a Facebook

“Ki Barni Na Sarara a Aurena”: Matashiya Ta Roki Budurwar Mijinta a Facebook

  • Wata mata yar Najeriya ta caccaki wata budurwa a Facebook, inda ta zarge ta da kwace mata mijinta
  • Ta saki hotunan budurwar a dandalin na soshiyal midiya sannan ta roke ta da ta barta ta sarara a gidan aurenta
  • Matar da ta shiga rudani ta zargi budurwar mijinta da kai shi wajen wani malami, inda aka sanar da shi cewa matarsa ce bara gurbi

Wata mata yar Najeriya mau suna Oluwakemisola Ajoke ta yi wa wata mata mai suna Lynn Omoshalewa Olaegbe wankin babban bargo a Facebook kan kwace mata miji.

A wani rubutu da aka goge a yanzu, Ajoke ta roki duk wanda ya san Omoshalewa da ya taimaka ya fada mata cewa ta bar mata aurenta.

Matashiya da hoton wallafar Facebook
“Ki Barni Na Sarara a Aurena”: Matashiya Ta Roki Budurwar Mijinta a Facebook Hoto: Oluwakemisola Ajoke
Asali: Facebook

Ta ce Omoshalewa uwar yara uku ce da ba ta da miji sannan ta koka cewa tana fuskantar matsaloli da dama a gidan aurenta.

Kara karanta wannan

“Bayan Shekaru 15 Da Aure”: Matar Aure Ta Koka a Bidiyo Yayin da Mijinta Ya Fada Mata Ita Ba Ajinsa Bace

Ta zargi matar da kai mijinta wajen malami, wanda ya fada masa cewa matarsa ce tushen rashin ci gabansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajoke ta ce ta shirya barin gidan auren amma ta yi gargadin cewa ba za ta tafi haka kawai ba.

Jama'a sun yi martani

Gracious Law ya ce:

"Menene dalilin da zai sa ta dauki mijin wata zuwa wajen malami babu wanda ke magana kan haka sai neman aibun baiwar Allah."

Helen Mike-Esohwode ta ce:

"Rayuwar soshiyal midiya ba tawa bace. Ba zan iya jinjinawa namiji ko na kiransa da sunaye msu dadi da bai cancance shi ba don kawai mutane su yarda cewa ina zaune lafiya. Sam ba da ni ba. Yana ta cin amanarki da yi maki dukan tsiya da dadewa amma kina da karfin halin jinjina masa a ranar zagoywar ranar hihuwarsa, hajiya je ki yi bacci tukuna, idan kin farka sai ki fada mun abun da kika gani."

Kara karanta wannan

Assha: Ta yi aure da nufin jin dadi, ta shiga rudani saboda halin mijinta dan wata jiha

Sweetpear Isieturugo ta ce:

"Mata ku daina yabon mazajenku da yawa a soshiyal midiya idan zai ci mutuncinki a wannan soshiyal midiya din ne zai ci mutunci da muzantaki "a wannan lokacin kunya ne zai zama sunanki na gaba....amma b za ku ji ba."

Matar aure ta koka bayan mijinta na shekaru 15 ya ce ita ba ajinsa bace

A wani labari na daban, wata matar aure ta koka a dandlin sohiyal midiya bayan mijinta da suka shafe tsawon shekaru 15 tare ya ce mata ita ba ajinsa bace.

Matar wacce ta samu karayar zuciya ta bayyana cewa Allah ya albarkace su da haihuwar 'ya'ya hudu a tsakanin wadannan shekaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel