Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Zamfara, Sun Sace 'Yan Mata 30

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Zamfara, Sun Sace 'Yan Mata 30

  • Miyagun ƴan bindiga sun sake kai munanan farmaki a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da ƴan mata fiye da 30 waɗanda suka shiga daji samo itacen da za a yi amfani da su
  • Ƴan bindigan sun kuma halaka mutane da dama ciki har da jami'an ƴan sakai da suka zo kawo ɗauki a wani ƙauye

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi awon da ƴan mata fiye da 30 a wani mummunan hari da suka kai a jihar Zamfara.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma halaka mutane masu yawa a harin da suka kai cikin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.

Yan bindiga sun sace 'yan mata 30 a jihar Zamfara
Yan bindigan sun sace yan matan bayan sun je yin itace Hoto: guardian.com
Asali: UGC

Miyagun ƴan bindigan sun kai farmakin ne a ƙauyuksn Janbako da Sakkida, a ranar Asabar, 3 ga watan Yunin 2023.

Maharan sun halaka mutum 20 a ƙauyen Sakkida sannan suka jikkata ƙarin wasu mutanen da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin ya yi bayanin cewa, ƴan bindiga sun ɗauki ƴan mata fiye da 30 a wani ƙauye mai suna Gora, lokacin da suka rafi dajin Daggera domin samo abun wuta.

Ya yi bayanin cewa tun farko sai da ƴan bindigan suka yi musu gargaɗin cewa idan suna su yi noma a Daggera a wannan shekarar, to sai sun yi sulhu da su. Ya ce ya yi mamakin sace yaran saboda sun yi sulhun kamar yadda suka buƙata.

Ya ci gaba da cewa har yanzu babu wani labari dangane da yaran, sai dai jami'an tsaro sun bi bayan ƴan bindigan duk da dai babu wani labari.

Ƴan bindigan sun yi musu kwanton ɓauna

Wani mazaunin ƙauyen Janbako, ya bayyana cewa suna cikin zamansu kawai sai ga saƙo ya zo daga Sakkida cewa suna son a kawo musu ɗauki miyagu sun shigo musu gari, cewar rahoton Premium Times.

Ya ce nan da nan mutanen ƙauyen tare da ƴan bijilanti suka rungumi makamai suka nufi ƙauyen Sakkida. Sai dai abinda ba su sani ba shi ne ƴan bindigan sun yi musu kwanton ɓauna, suna shiga gsrin suka buɗe musu wuta inda mutane da dama suka halaka.

Ya ci gaba da cewa a ƙauyensu kawai sai da aka binne gawarwakin mutum 22 bayan an yi musu sallah.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutane Da Dama a Kauyukan Jihar Benue

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun kai mummunan hari a wasu ƙauyukan jihar Benue, inda suka halaka mutane da dama.

Ƴan bindigan sun halaka mutane sama da 20 sannan wasu da dama sun jikkata, yayin da suka ƙona gidaje masu yawa..

Asali: Legit.ng

Online view pixel