'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane Da Dama a Kauyukan Jihar Benue

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane Da Dama a Kauyukan Jihar Benue

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da juna cikin jihar Benue a yankin Arewa ta tsakiya
  • Ƴan bindigan sun kutsa cikin wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Katsina-Ala kan babura inda suka halaka aƙalla mutum 25
  • Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana maharan tsagerun ƴan bindiga ne na yankin ba Fulani makiyaya ba

Jihar Benue - Ƴan bindiga sun farmaki ƙauyen Imande Mbakange da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da shi a mazaɓar Mbacher, cikin ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa aƙalla mutum 25 ne suka halaka, wasu da dama sun raunata sannan ƴan bindigan sun ƙona gidaje masu yawa.

Yan bindiga sun halaka mutum 25 a jihar Benue
'Yan bindigan sun isa kauyakun ne a kan babura Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

A cewar wani mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan, ƴan bindigan sun shiga ƙauyukan ne a kan babura da safiyar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sake Sace 'Yan Mata Masu Yawa a Jihar Zamfara

Mutumin wanda ya bayyana sunan shi a matsayin Terwase, ya bayyana cewa ƴan bindigan da suka zo kawo harin suna da ɗumbin yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ƴan bindigan sun zo ne da yawa a kan baburansu sannan suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan ya sanya suka halaka mutane da dama." A cewarsa.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Atera Alfred, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa ƴan bindigan da ke a yankin sune suke da alhakin kawo harin, rahoton Punch ya tabbatar.

"Eh da gaske ne, ranar Asabar da safe wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Imande Mbakange da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da shi a mazaɓar Mbacher. Ƴan bindigan ba Fulani makiyaya bane."

Shugaban ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa yankin, inda har an faro gano wasu daga cikin gawarwakin.

Kara karanta wannan

Ba Sauki: 'Yan Ta'addan ISWAP Sun Nutse Cikin Kogi a Kokarin Tserewa Luguden Wuta Na Dakarun Sojoji a Borno

Ya zuwa lokacin da aka tunutuɓe ta, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta yi cikakken bayani ba.

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Nutse Cikin Ruwa

A wani rahoton na daban kuma, wasu ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP sun baƙunci lahira bayan sun nutse a cikin.

Ƴan ta'addan dai na ƙoƙarin tserewa ne daga luguden wutan da dakarun sojoji suke musu a maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel