Abin Al’ajabi: Bidiyon Wasu Wadanni Mata da Miji Na Ba Hammata Iska Ya Dauki Hankalin Jama’a

Abin Al’ajabi: Bidiyon Wasu Wadanni Mata da Miji Na Ba Hammata Iska Ya Dauki Hankalin Jama’a

  • A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an gano wasu wadannin ma’aurata a lokacin da suke ba hammata iska
  • Matar, wacce alamu ke nuna tana da ciki ta gargadi mijin nata a lokacin da suke fada kana ta ture shi a gefe
  • Ganin yadda ta dawo daidai a lokacin da ta fadi a kasa, mutane da yawa sun shiga mamaki, sun bayyana ra’ayoyinsu

Wata mata mai karamin jiki da gajerta ta gargadi mijinta a lokacin da suka barke da fada a cikin gida, fadan da ya ba mutane da yawa mamaki.

A wani bidiyon da ya yi shuhura a kafar sada zumunta, mata da mijin, wadanda duk wadanni ne sun yi fada mai ban dariya.

Da fari ture mijin nata ta yi a kasa, kana ta naushe shi a baya kamar wacce ke fada da sa’anta; amma ta fadi kasa.

Yayin da mijin ke kan gwiwarsa daya, nan da nan ita kuwa ta tashi ba tare da dafa kasa ba, lamarin da ya ba mutane mamaki.

Fadan wada da matarsa ta ba da annashuwa
Yadda mata da miji ke fada a cikin daki | Hoyo: @KhaySleek
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan, matar ta kama kugu tana kuma tsayuwar fada kamar wacce ta yi damara kana ta fice daga wurin da mijin ke tsaye. Mutane da yawa a kafar zumunta sun yi mamaki.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@Clementscalar:

“Mutanen nan suna da kira ta daban.
“Kalli yadda ta tashi ba tare da dafa komai ba.
“Eeeei.”

@ola_bukun:

“Omo! Allah mai halitta kalli yadda ta tashi ba tare da rike komai ba.”

@stevewest223456:

“Tambayata anan ita ce na ga tana da juna biyu amma bata da nono. Ta yaya za ta shayar da jajirinta?”

@OlamilekanChad:

“Meye wannan, wadannan sun yi kama da minions a ido na.”

@bayo_alabi_:

“Kawai kalli yadda ta tashi da kuma yadda ta bar wuri, dariya kamar za ta kashe ni.”

@__arike_adey:

“Yadda ta tashin nan abin ban mamaki ne, bidiyonsu na TikTok na da ban dariya da kyau wani lokacin.”

@insanespotter:

“Yadda ta tashi ne ya bani mamaki.”

@AllStackDev:

“Meye tabbacin za ta iya haifar wada?”

Yadda aure ke gara wata mata a Anambra

Wata mata ta bayyana yadda aure ya kaita jihar Anambra da kuma yadda take shan wahala a madadin ta ji dadi.

A cewarta, tana neman shawarin yadda ake ji da maza 'yan jihar Anambra, jama'a sun ba ta shawarin da ya dawce.

Rayuwar aure na daya daga abubuwan da mutane a Najeriya ke yawan fuskantar matsala a kai duba da yadda zamantakewa ke kara lalacewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel