Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

  • Yusuf Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, ya ce rantsar da Bola Tinubu ya saɓa wa kundin tsarin mulki
  • Ya bayyana cewa duk da rantsar da shi da za ayi kotu ce kawai ke da hurumin tabbatar da shi a matsayin shugaban ƙasa
  • Datti Baba-Ahmed ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su zama masu bin doka da oda, inda ya yi nuni da cewa gaskiya ta kusa yin halinta

Jihar Kaduna - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed, ya sake nanata cewa da shi da Peter Obi ne suka lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023, sannan rantsar da Bola Tinubu ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Datti ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan ya halarci wani ɗaurin aure masallacin Sultan Bello, da ke Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Peter Obi Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Obidients' Da Sauran 'Yan Najeriya

Datti Baba-Ahmed ya aike da sako kan rantsar da Tinubu
Datti Baba-Ahmed ya ce rantsar da Tinubu ya saba ka'ida Hoto: Yusuf Datti Baba-Ahmed, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A kalamansa:

"Kada mu manta cewa mu ƴan ƙasa ne masu bin doka da oda waɗanda ba za su yi wa gwamnati bore ba. Kamar yadda na sha faɗi, Allah shine mai ƙarfin iko, gwamnati ta biyo daga baya. Idan ta zaɓi ta yi adalci, za ta yi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun bayyana cewa mun yarda an yi mana rashin adalci a zaɓen da ya wuce. Doka ta ba mu damar mu nemi haƙƙinmu a kotu, kuma muna jiran a ƙwato mana haƙƙinmu, haƙƙin ƴan Najeriya."
"Da ni da Peter Obi mu ka lashe zaɓen nan, sannan indai akwai adalci a Najeriya, da yardar Allah, za mu shugabanci Najeriya sannan mu gyara ta."

Rantsar da Bola Tinubu ba zai sanya su sare ba

Ya kuma yi nuni da cewa duk da rantsar ɗa Bola Tinibu da za ayi, hakan ba zai hana su ƙoƙarin ƙwato haƙƙinsu ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Ya Sauya a Najeriya Daga 2015 Zuwa 2023

Datti ya bayyana cewa rantsar da Bola Tinubu, zai ƙara musu ƙarfi ne maimakon ya sanya guiwoyinsu su yi sanyi.

Peter Obi, wanda shi ma ya yi magana da manema labaran a wajen ɗaurin auren, ya ce kotu ce kawai za ta tabbatar da sahihancin rantsar da Bola Tinubu.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su zauna cikin kwanciyar hankali da juna, sannan su kasance masu bin doka da oda, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Zanga-Zanga a Eagles Square

A wani rahoton na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana cewa ba zai halarci bikin rantsar da Bola Tinibu ba.

Peter Obi ya kuma musanta cewa magoya bayansa za su gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da rantsar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel