Jirgin Saman Najeriya Ya Koma Jigilar Fasinjoji Kamar Yadda Bincike Ya Nuna

Jirgin Saman Najeriya Ya Koma Jigilar Fasinjoji Kamar Yadda Bincike Ya Nuna

  • Kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines ya cire sunan Najeriya daga jikin jirginsa sannan ya koma hada-hadarsa
  • Jirgin wanda mallakin Ethiopian Airlines ne, ya koma kamfanin bayan ya wakilci kamfanin Nigeria Air a takaice
  • Har yanzu kamfanin Ethiopian Airlines da gwamnatin Najeriya basu bayyana dalilin yi wa jirgin kwaskwariman na wucin gadi ba

Kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines ya cire fenti da sunan 'Nigeria Air' daga jikin jirgin da aka nuna a matsayin na kamfanin jirgin saman Najeriya.

A cewar wata na'urar bin diddigi, yanzu kamfanin Ethiopian Airlines na amfani da wannan jirgi wajen gudanar da ayyukansa.

Jirgin Najeriya ya koma Habasha
Jirgin Najeriya da aka kaddamar kwanan nan | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

An sake wa jirgin, na kamfanin Boeing 737-800 mai rijista ET-APL fenti da suna don ya wakilci kamfanin jirgin saman Najeriya kamar yadda ministan sufurin jirgin sama na Najeriya, Hadi Sirika ya bukata.

Sai dai kuma, tuni aka mayarwa ainahin mamallakinsa wato Ethiopian Airlines, rahoton jaridar Business Day.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina jirgin saman Najeriya

Bayanin jirgin daga wata na'urar bin diddigi ya nuna cewa a ranar Laraba, 30 ga watan Maris din 2023, jirgin ya tashi daga Addis Ababa sannan ya lula zuwa Mogadishu.

Daga bisani a wannan yammacin ya koma Addis Ababa.

Wani dan jarida mai zaman kansa David Hundeyin ya ja hankalin jama'a zuwa ga na'urar jirgin ta shafinsa na Twitter, yana mai cewa an cire sabon sunan da aka sa wa jirgin saman na Najeriya sannan ya koma bakin aikinsa na jigila tsakanin Addis Ababa-Magadishu.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa bayanai daga na'urar bin diddigi na jirgin, 'flightradar24.com'ya nuna cewa jirgin Najeriyan ya koma inda ya fito a kasar Habasha.

Jirgin ya koma Habasha

Na'urar ta kuma nuna jirgin saman ya tashi daga Najeriya zuwa kasar Habasha.

Bayanai game da binciken da aka yi kan tarihin jirgin ya nuna cewa kimanin shekaru 11 kenan ya fara aiki.

Ya fara tashinsa na farko a ranar 22 ga watam Yunin 2012 karkashin kamfanin Ethiopian Airlines.

Daga bisani ya yi aiki karkashin sunan Malawi Airlines daga ranar 16 ga watan Fabrairun 2014 kafim aka mayar da shi kamfanin Ethiopian Airlines a ranar 12 ga watan Agustan 2015.

Duk da sauya kaloli daaka yi, sunan mamallakin jirgin na nan a matsayin Ethiopian Airlines.

Idan baku manta ba, an bayyana sanar da fara aikin jirgin ne kwanaki kadan kafin shugaba Buhari ya mika mulki ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel