Kamfanin Jirgin Najeriya Zai Fara Aiki Kafin Buhari Ya Sauka a Mulki, Inji Minista Sirika

Kamfanin Jirgin Najeriya Zai Fara Aiki Kafin Buhari Ya Sauka a Mulki, Inji Minista Sirika

  • Hadi Sirika ya ba yan Najeriya tabbacin cewa jirgin saman kasar wato 'Nigeria Air' na gab da fara aiki
  • Ministan sufirin jiragen sama na kasar ya bayyana cewa kamfanin jirgin Najeriya zai fara aiki kafin Buhari ya mika mulki ga gwamnatin gaba
  • Ya bayar da tabbacin ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris a taron masu rua da tsaki da ya gudana a Abuja

Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya sanar da cewar kamfanin jirgin sama na kasa, 'Nigeria Air' zai fara tashi kafin ranar 29 ga watan Mayun 2023, rahoton The Nation.

Ministan ya kuma bayyana cewa kaso 98 cikin 100 na aikin ya kammala.

Jirgin Nigeria Air na kasa
Yanzu Yanzu: Jirgin 'Nigeria Air’ Zai Fara Tashi Kafin 29 ga Watan Mayu – Sirika Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris a wajen taron kungiyar masu ruwa da tsaki kan harkar sufurin jiragen sama na 10.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kama wasu da ke sace yara da sunan za su kaisu gidan marayu a jihar Arewa

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jirgin saman zai fara tashi kafin ranar 29 ga watan Mayun shekarar nan."

Babu gwamnatin da ta tallafawa kamfanonin jiragen gida kamar ta Buhari, minista

Ya ce gwamnatin tarayya na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalolin da kamfanonin jiragen saman gida da suka garzaya kotu don dakatar da tsarin suka kwanto.

Ministan ya bayyana matakin da jiragen saman gidan suka dauka a matsayin rashin adalci, yana mai cewa gwamnatin Buhari ta tallafawa jiragin gida fiye da gwamnatocin baya, Daily Trust ta rahoto.

Ya zarge su da kawo karan tsaye ga tabbatuwar kamfanin jirgin kasar wanda zai samar da sabbin ayyuka da damammaki masu kyau a harkar

Yadda za a yi rabe-raben kamfenin

Idan za ku tuna, a baya ministan sufurin jiragen ya bayyana cewa kamfanin jirgin na kasa zai hada kai da wani kamfani, inda gwamnati za ta rike kashi biyar cikin 100 na kamfanin.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Har ila yau, yan kasuwa za su rike kaso 46 sannan sauran kaso 49 za a bayar da su ga abokan huldar hada-hadar da za su hannun jari da suka hada da masu zuba jari na kasashen waje.

Hakazalika, Sirika ya ce idan har kamfanin ya fara aiki, zai samar da ayyukan yi kimanin 70,000 ga al’ummar Najeriya.

Ya ce ma’aikatar sufurin jiragen saman Najeriya ita kadai ce a duniya za ka samu kwararrun matukan jirage amma babu aikin yi.

Ya ce matukan jiragen sama 50 sun zo gare shi suna korafin rashin aikin yi, yana mai cewa kamfanin jirgin saman na kasa zai dauki karin matukan jirage aiki da kuma samar da wasu ayyukan.

Yan siyasar Najeriya ne suka jefa kasar a matsala - Fayose

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya daura laifin halin da kasar ke ciki a yanzu kan yan siyasa da masu rike da madafun iko.

Fayose ya ce tun daga shekarar 1979 babu wani abu guda daya da ya sauya cewa lamarin ci gaba na ta tafiyar hawainiya a kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel