Rashin Da’a: Rundunar ’Yan Sanda Ta Kori Sajan Bisa Zargin Damfarar Matashi N98,000

Rashin Da’a: Rundunar ’Yan Sanda Ta Kori Sajan Bisa Zargin Damfarar Matashi N98,000

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta sanar da korar Sajan Ekpo Shimuyere bisa zargin damfarar wani matashi
  • Kakakin rundunar a jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba
  • Ya ce tsohon dan sandan ya yi amfani da na'urar cire kudi ta POS ya cire makudan kudade har N98,000.

Jihar Lagos – Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta sanar da korar Sajan Ekpo Shimuyere da ke ofishin ‘yan sanda na Sogunle bisa zargin karbar kudi har N98,000 a hannun wani matashi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba 31 ga watan Mayu.

An kori dan sanda saboda samunsa da damfarar wani a Legas
Dan sanda mai mukamin saja ya rasa aikinsa saboda damfarar wani N98,000 a Legas. Hoto: Pulse.ng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce tsohon jami’in dan sandan da aka kora ya karbi wayar hannun matashin tare da cire kudi N98,000 daga cikin N100,000 da ke asusun bankin matashin ta hanyar amfani da na'urar cire kudi ta POS.

Kakakin Yan Sanda Hundeyin ya ce aikata hakan ya sabawa dokokin 'yan sanda

Hundeyin ya ce aikata hakan ya saba wa dokokin hukumar ‘yan sanda ta Najeriya, cewar Daily Nigerian.

A cewarsa:

“Hukumar ‘yan sanda ta samu korafi daga wanda aka damfara, amma sai dan sandan ya musa zargin da ake masa, rundunar ta kulle dan sandan saboda kada ya kawo cikas a shaidun da ake da su.
“Mun samu bayanin shige da ficen kudi daga bankinsa, mun yi nasarar gano kudaden inda muka ga yadda aka tura kudaden zuwa asusun bankinsa.
“Mun bi hanyar da ya dace na bincike kuma muka gayyace shi don bincike yayin da ya tabbatar ya aikata hakan."

Ya kara da cewa:

“Mun kuma gayyaci matashin, inda ya ce dan sandan ne ya bukaci ya tura masa kudin zuwa asusun bankin.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idowu Owohunwa ya bukaci ya duba tsarin yadda aka gudanar da binciken, sannan ya amince da hukunta jami’in ta hanyar kora daga aiki."

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya ja kunnen jami'ansa

Mista Hundeyin ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ya gargadi jami’an ‘yan sanda da su guji karbar cin hanci da rashawa, inda ya ce wannan korar zai zama izina ga sauran jami’an, cewar Tribune.

Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bisa Zargin Halaka Mahaifiyarsa a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Kano sun yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da kashe mahaifiyarsa.

Matashin mai suna Ibrahim Musa ana zargin ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 50 a Rimin Kebe da ke karamar hukumar Ungogo a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel