An Buga an Dawo: Kotu Ta Mayar da Muhuyi Kan Kujerarsa Ta Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano

An Buga an Dawo: Kotu Ta Mayar da Muhuyi Kan Kujerarsa Ta Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano

  • Kotun masana’antu ta kasa da ke jihar Kano ta ba da umarnin a maida Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rahawa
  • Tsohuwar gwamnati da majalisar jihar ne suka shigar da kara don a sauke Muhuyi a matsayinsa bisa wasu korafe-korafe da ake tuhumarsa akansu
  • Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Ebeye David ya ce ba a bi ka’ida ba a sauraran karar, kuma majalisar ba ta da hurumin sallamarshi a mukaminsa

Jihar Kano – Kotun Masana’antu ta kasa da ke jihar Kano ta ba da umarnin a maida Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (PCACC) ta jihar Kano ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin jihar Kano da majalisar jihar ne suka shigar da karar Muhuyi da neman kotun da sauke shi daga matsayinsa.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

Muhuyi Magaji
Kotu Ta Mayar da Muhuyi Kan Kujerarsa Ta Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano, Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Ebeye David Eseimo ya ce ba a yi wa wanda ke karar adalci a sauraran karar ba kuma majalisar jihar ba tada hurumin korarshi a matsayin.

Ya kara da cewa majalisar ba da ta wannan karfin iko ba tare da yin adalci ga ko wane bangare a sauraran karar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Shari'a ya ce ba a bi ka'ida ba wajen cire Muhuyi a mukaminsa

Mai Shari’an ya ce an sallami Muhuyi daga mukaminsa ta hanyar da bata dace ba, don haka kotun ta ba da umarnin mayar da shi mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Daily Trust ta tattaro cewa an dakatar da Muhuyi daga mukaminsa, kafin daga baya tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya sallame shi gaba daya a mukamin nasa.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Tsohon gwamna Ganduje ya cire shi ne a mukamin nasa bayan majalisar jihar ta bankado cewa akwai zarge-zarge da korafi da dama da ake tuhumarsa akansu, cewar jaridar Tribune.

Muhuyi a nasa bangaren, ya fada wa ‘yan jaridu cewa tsohuwar gwamnatin Ganduje ta cire shi ne a mukaminsa saboda yana binciken wata badakala ta manyan ayyuka da ya shafi iyalan gwamnan.

Kotu ta Mayar Wa Muhyi RiminGado Kujerarsa, Tace Ganduje Ya Biya Shi Albashinsa

A wani labarin, kotun masana'antu ta kasa ta tabbatar da Muhuyi Magaji a matsayin shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano.

Kotun ta umarci gwamnatin Ganduje ta biya Muhuyi dukkan alawus da kuma albashinsa da ta rike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel