Kotu ta Mayar da Muhyi RiminGado Kujerarsa, Tace Ganduje Ya Biya Shi Dukkan Albashinsa

Kotu ta Mayar da Muhyi RiminGado Kujerarsa, Tace Ganduje Ya Biya Shi Dukkan Albashinsa

  • Kotun masana'anta ta kasa ta tabbatar da dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano, Muhyi Rimingado a matsayin shugaban hukumar
  • Hakan yazo ne bayan maka gwamnatin jihar Kano da yayi a watan Yulin shekarar da ta gabata bisa dakatar dashi na wata daya da tayi
  • Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya shi dukkan albashi da alawus dinsa a yayin da aka dakatar dashi domin hakkinsa ne

Kano - Kotun masana'antu ta kasa dake Abuja ta tabbatar da shugaban hukumar yaki da rasha ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, wanda aka dakatar a matsayin Shugaban hukumar.

Muhyi Rimingado
Kotu ta Mayar da Muhyi RiminGado Kujerarsa, Tace Ganduje Ya Biya Shi Dukkan Albashinsa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kotu Tace a biya shi albashi

Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya Magaji albashinsa da alawus din da ta rike masa bayan dakatar da shi a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

Magaji ya shigar da kara kotu akan soke dakatar da shi da aka yi, Premium Times ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An dakatar da shi na tsawon wata daya a watan Yulin 2021 bisa rashin amincewa amsar wani akawun hukuma daga ofishin akawu-janar na jihar.

Kotun ta ayyana cewa har yanzu Magaji yana nan a matsayin shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar tare da umartar Abdullahi Ganduje ya cigaba da biyansa albashinsa da alawus na N5,713,891.22.

Yayin gabatar da shari'ar a ranar Laraba, Alkali Oyebia Oyewumi, ya ce Magaji yana da alhakin a biyasa albashinsa duk karshen wata daga ranar da aka kammala shari'a zuwa lokacin da za'a maido da shi bakin aikinsa.

Sai dai, alkalin ya ki amsar bukatar Magaji na ayyana dakatar da shi a matsayin abun da bai dace ba gami da soke shi.

Kara karanta wannan

Na Yi Iya Abun da Zan Iya a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya, Buhari

An tauyewa Rimingado hakkinsa, Alkali

Sai dai, alkalin ya ce tauye hakkin mai daukar aiki ne kin bashi damar hukunta wanda ya dauki aiki, duba da gwamnati ce ta dauke shi.

Kotun ta ce, gwamnati na da damar dakatar da shi, kuma yin hakan zai iya ko kin bashi damar jin ba'asin dakatar da shi, dalili kuwa shine dakatarwa ba tauye hakki bane na dindindin, ba kamar kora ba wacce ke bama wanda aka dauka aiki jin ba'asi.

Haka zalika, kotun ta dora laifi ga rundunar 'yan sandan jihar Kano bisa kama Magaji tare da lasisin kama mutum, wacce bata bayyana wani laifi ba, inda kotun take ganin hakan ba daidai bane a shari'ance, sannan ta hana kwamishinan 'yan sandan wanda yake jeri na shida cikin wadanda ake kara daga shiga lamarin wanda yayi karar a kowanne abu da ya shafi wajen aikinsa.

Har zuwa yanzu, gwamnatin jihar Kano ba tayi martani game da lamarin ba, yayin da a safiyar Juma'a aka yi kokarin tuntubar wayar kakakin gwamnatin jihar, Muhammad Garba don jin ta bakinsa bata shiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel