Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Umarci Jami'an DSS Da Su Bar Ofishin EFCC Cikin Gaggawa

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Umarci Jami'an DSS Da Su Bar Ofishin EFCC Cikin Gaggawa

  • Sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su fice daga ofishin EFCC da suka mamaye
  • A safiyar ranar Talata ne dai jami'an na DSS suka mamaye ofishin jami'an EFCC da ke Ikoyi Legas, inda suka hana su gudanar da ayyukansu
  • Tinubu ya bayar da umarnin ne ta hannun mai magana da yawunsa Tunde Rahman, inda ya bayyana cewa za a sulhunta hukumomin cikin ruwan sanyi

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) da su bar ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da ke Ikoyi, Legas cikin gaggawa.

A labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, mun kawo muku cewa jami'an hukumar DSS sun yi wa ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ƙawanya da safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS Sun Mamaye Ofishin EFCC Na Legas, Sun Hana Jami’an Shiga Ofis

Tinubu ya umarci DSS su fice daga ofishin EFCC
Shugaba Tinubu ya umarci jami'an DSS da su fice daga ofishin EFCC cikin gaggawa: Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

Jami'an DSS sun tare hanyar shiga ofishin

Bayan haka, jami’an na farin kaya, a cikin wasu motoci guda biyu masu ɗauke da makamai, sun tare babbar kofar shiga ofishin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin hukumomin guda biyu kan batun mallakin ginin ofishin.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, da aka tuntuɓe shi, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin wani baƙon abu.

Ya bayyana cewa hukumomin biyu sun zauna tare a cikin ginin na sama da shekaru 20 ba tare da wata ɓaraka ba.

DSS ta yi iƙirarin cewa ofishin na ta ne

Sai dai a wani martani da ya mayar, kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya, ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa, ginin da ake magana a kai na hukumar DSS ne, don haka ba daidai ba ne a ce jami’ansu sun yi wa ofishin EFCC shinge.

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Tunde Rahman, ya fitar a madadinsa a yammacin ranar Talata, Tinubu ya ce za a warware matsalar da ke tsakanin hukumomin biyu cikin ruwan sanyi, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Sanarwar na cewa:

“Shugaba Bola Tinubu ya umarci jami'an hukumar tsaro ta ƙasa (DSS), da su gaggauta ficewa daga ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da ke Ikoyi, Legas.”
“Shugaban ya bayar da umarnin ne a lokacin da aka kawo masa rahoton cewa jami’an DSS sun kai farmaki ofishin EFCC da ke kan titin Awolowo, Ikoyi, Legas a ranar Talata, inda suka hana jami’an hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa isa wurin aikinsu.”
"Shugaban ya ce idan ma akwai matsala tsakanin manyan hukumomin guda biyu, za a warwareta cikin ruwan sanyi."

An buƙaci EFCC su hana muƙarraban gwamnatin Buhari fita waje

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

A wani labarin mu na baya, gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG) ta buƙaci hukumar EFCC ta hana muƙarraban gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari guduwa zuwa ƙasar waje.

Ƙungiyar ta buƙaci hukumar ta hana waɗanda ake zargi da ayyuka na cin hanci da rashawa a cikin muƙarraban na Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel