Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsarin 'Ba Aiki Ba Biyan Albashi' Tsakanin FG Da ASUU

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsarin 'Ba Aiki Ba Biyan Albashi' Tsakanin FG Da ASUU

  • Kotun ma'aikata ta kawo karshen karar da gwamnatin tarayya ta shigar da ASUU kan tsarin ba aiki ba biyan albashi
  • Alkalin Kotun ya ce FG na da ikon riƙe albashin dukkan ma'aikatan da suka tsunduma yajin aiki
  • Haka nan kuma Kotu ta bai wa ASUU gaskiya game da batun biyan albashi ta hanyar amfani da tsarin IPPIS

Abuja - Kotun ɗa'ar ma'aikata ta amince da tsarin 'Ba aiki ba biyan albashi,' wanda gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba wa malaman ƙungiyar jami'o'i (ASUU) a lokacin da suka tsunduma yajin aiki.

Channels TV ta tattaro cewa Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ƙarar da FG ta shigar da ƙungiyar ASUU kan tsarin ba aiki ba biya.

Gudumar Alkali.
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsarin 'Ba Aiki Ba Biyan Albashi' Tsakanin FG Da ASUU Hoto: channels
Asali: UGC

A cewar Kotun, tsarin rashin biyan albashi da gwamnatin tarayya ta sanya wa ASUU lokacin da take yajin aiki a shekarar da ta gabata, ya halatta kuma bata saɓa doka ba.

Da yake yanke hukunci kan ƙarar, Alkalin Kotun mai shari'a Benedict Kanyip, ya ce doka ta bai wa FG ƙarfin ikon riƙe albashin duk wani ma'aikacin da ya shiga yajin aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu ta yanke hukunci kan IPPIS

Haka nan kuma Kotun ta yanke cewa bai halatta FG ta tilasta amfani da tsarin biyan albashi IPPIS wajen biyan malaman Jami'a haƙƙoƙinsu ba, ta ce hakan ya saɓa wa dokar cin gashin kan jami'o'i.

A cewar mai shari'a Benedict Kanyip, Malaman jami'o'in tarayya suna da 'yancin zaɓen hanyar da gwamnati zata bi wajen biyansu albashi.

Meyasa FG ta kai ƙarar ASUU gaban Kotu?

Tun usuli, gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar ASUU gaban Kotun ɗa'ar ma'aikata saboda ta buƙaci a biya mambobinta albashinsu na watanni 9, kamr yadda Daily Trust ta ruwaito.

FG ta ce ASUU ta nemi gwamnati ta biya malaman jami'o'in tarayya albashinsu na tsawon lokacin da suka shafe suna yajin aiki tsakanin 14 ga watan Fabrairu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2022.

"Tallafin Mai Ya Tafi" Shugaba Tinubu

A wani labarin na daban kuma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da shirinsa na cire tallafin kan fetur a Najeriya.

Tinubu ya sha alwashin karkatar da kuɗin tallafin zuwa bangaren ilimi, noma da kiyo, kiyon lafiya da sauran ayyukan raya ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel