Ortom Ya Yi Martani Yayin da Rahoton Shirin EFCC Na Kama Shi Ya Dauka Hankali

Ortom Ya Yi Martani Yayin da Rahoton Shirin EFCC Na Kama Shi Ya Dauka Hankali

  • Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi watsi da rahoton cewa hukumar EFCC ta kama shi
  • Terver Akase, hadimin labaran gwamnan, ya yi watsi da rahoton sannan ya cewa oRtom zai gabatar da kansa ga EFCC ko wata hukumar yaki da rashawa idan aka gayyace shi
  • Akase a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa Ortom ya sha fadin cewa ya tafiyar da gwamnati cikin gaskiya kuma ba shi da abun boyewa

Benue - Samuel Ortom, tsohon gwamnan jihar Benue, ya yi martani kan rahotannin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na shirin kama shi.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Terver Akase, hadimin labaran tsohon gwamnan Ortom, ya karyata rahoton, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Uba Sani Ya Nada Mukarraban Tsohon Gwamna El-Rufai Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

Hukumar EFCC da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
Ortom Ya Yi Martani Yayin da Rahoton Shirin EFCC Na Kama Shi Ya Dauka Hankali Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Twitter

Me yasa EFCC ke bibiyan tsohon Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue

A cewar Akase, toshon gwamnan bai da "wani abun boyewa", yana mai cewa tsohon gwamnan ya tafiyar da gwamnati ta gaskiya a matsayin gwamnan jihar Benue.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ta hannun hadiminsa ya kuma bayyana shirinsa na amsa kowace gayatta daga hukumar EFCC ko wata hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ke bukatar karin bayani game da lokacin da ya kwshe a matsayin gwamnan jihar Benue.

Akase ya ce rahoton da wasu jaridun yanar gizo, ba legit.ng ba suka wallafa, bai da tushe kuma ba gaskiya bane.

Wani bangare na jawabin ya ce:

"Yana da kyau a bayyana cewa mai Girma Samuel Ortom bai da abun boyewa kuma zai gabatar da kansa a duk lokacin da EFCC ta gayyace shi."

Kara karanta wannan

Ganawar Tinubu da Kwankwaso: Ganduje Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Tinubu Ya Bashi Mukami

Ortom na daya daga cikin manyan gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka yi kira ga mika mulki ga yankin kudu a jam'iyyar adawar.

Kuma ya goyi bayan takarar Peter Obi na Labour Party bisa ga dan takarar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar.

Ya sha kaye a kokarinsa na son zama sanata kuma PDP ta fadi zaben gwamnan jihar inda APC ta yi nasara a zaben na 2023.

Buhari ya gaza sosai kuma dole a fada masa, Ortom

A baya mun kawo cewa Samuel Ortom ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari wankin babban bargo cewa gwamnatinsa ta gaza sosai.

Ortom ya ce ba a taba yin lalatacciyar gwamnati kamar ta Buhari ba a tarihin Najeriya kuma ya zama dole a fada masa gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel