Uba Sani Ya Nada Mukarraban Tsohon Gwamna El-Rufai Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

Uba Sani Ya Nada Mukarraban Tsohon Gwamna El-Rufai Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ba da sabbin mukamai a gwamnatinsa wanda mafi yawa sun rike mukamai a gwamnatin Nasiru El-rufai
  • Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Muhammad Lawal Shehu ne ya bayyana haka ne a wata sanarwa da gwamnan ya sanyawa hannu
  • Gwamnan ya nada Mallam Balarabe Abbas a matsayin sakataren gwamnati, wanda shi ne tsohon sakataren gwamnati a mulkin El-rufai

Jihar Kaduna – Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya nada manya-manyan mukamai da za su maye gurbin wurare masu muhimmanci da dama a gwamnatinsa.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar ya ce gwamnan ya bayyana cewa ya sake rike tsohon sakataren gwamnatin jihar na mulkin Nasiru El-rufai, Mallam Balarabe Abbas Lawan a mukaminsa na da.

Kara karanta wannan

Ganawar Tinubu da Kwankwaso: Ganduje Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Tinubu Ya Bashi Mukami

Tsohon gwamna El-rufai da Gwamna Uba Sani
Uba Sani Ya Nada Tsoffin Mukarraban Tsohon Gwamna El-Rufai, Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya rike shi a gurbin na shi na da ne saboda irin kwarewar da yake da shi wurin gudanar da gwamnati yadda ya dace.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Uba Sani ya kuma rike wasu jiga-jigai na gwamnatin Nasiru El-rufai saboda samun mahadi da zai dinke gwamnatocin guda biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda aka bai wa mukman sun hada da Muhammad Hafiz Bayero wanda shi ne ya zama babban mai bada shawara ga gwamnan da Barista James Atung da Chris Umar wadanda aka nada a matsayin mataimakan shugaban ma’aikata.

Sauran sun hada da Dakta Shehu Usman da Bulus Banquo Audu a matsayin masu bada shawara ga gwamnan, cewar rahotanni.

A cewar sanarwar:

“Gwamna Uba Sani ya amince da nadin sabon shugaban ma’aikata, Sabo Liman, wanda ya kasance kwararre a fannoni da dama na aiki.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Kama Gwamnan PDP Bayan Mika Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

“Ya kasance shi ne tsohon shugaban hukumar shige da fice reshen jihar Kano, kafin a dawo da shi jihar Kano, ya rike shugaban hukumar shige da ficen reshen jihar Kaduna.”

Gwamnan ya ce dukkan wadannan nade-nade an zabe su ne bayan duba kwarewarsu ta bangarori da dama wanda jihar take matukar bukatarsu don ci gaba da kawo sauyi da kuma dorewar wannan sabuwar gwamnati.

Ya bukaci wadanda suka samu wannan da suyi amfani da mukamin nasu wurin kawo wa jihar ci gaba saboda mutanen jihar suna matukar bukatar su a wannan lokaci.

Zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani Ya Yi Nadinsa Na Farko

A wani labarin, Zababben gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya sanar da Muhammad Lawal a matsayin sakataren yada labarai.

Gwamnan ya ce ya yi wannan nadin ne ganin yadda Muhammad Lawal ya ke da kwarewa ta bangarori daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel