Babbar Magana: Sabon Gwamnan Neja da Aka Rantsar Ya Ba da Umarnin Rusa Ofishin ’Yan Sanda

Babbar Magana: Sabon Gwamnan Neja da Aka Rantsar Ya Ba da Umarnin Rusa Ofishin ’Yan Sanda

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago ya bayyana cewa, zai rushe wani ofishin ‘yan sanda a jiharsa
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da ake rantsar dashi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, inji rahotanni
  • A yau ne aka rantsar da gwamnoni da shugaban kasar Najeriya bayan kammala zabuka a kasar

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja Mohammed Bago ya bayyana shirin rusa ofishin ‘yan sanda na Chanchaga da ke birnin Minna.

Bago ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin rantsar dashi a filin baje kolin kasuwanci na Minna a ranar Litinin, Punch ta ruwaito.

Bago ya sanar da cewa aiki na farko da zai fara shine sanya ofishin ‘yan sandan a layin rugujewa duk da bai bayyana yaushe za a yi ba.

Mohammed Bago ya ce zai rushe ofishin 'yan sanda
Mohammed Bago, gwamnan jihar Neja | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Dalilin da yasa za a ruguje ofishin ‘yan sandan

Ya nuna damuwarsa ga yadda ginin ofishin ‘yan sandan ke dakile bututun ruwa a yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa za a sanya wa ginin ofishin alamar rushewa nan take bayan kammala dukkan shirye-shirye.

"Za a ba da fifiko ga samar da ruwan sha mai tsafta, yayin da muka bar wannan wurin, muna da ofishin 'yan sandan da ke zaune a kan bututun ruwanmu, za mu sanya masa alamar rushewa saboda dole ne mu samar da ruwan sha ga mutanenmu."

Za mu magance matsalar tsaro, inji Bago

Ya kuma tabbatar wa da al’umma kudurin gwamnatinsa na magance matsalar rashin tsaro a jihar da kewaye, rahoton Channels Tv.

Hakazalika, ya kuma jaddada muhimmancin lamarin, inda ya yi alkawarin kiyaye ka’idar tsaro daidai yadda tsarin mulkin kasa ya tanada da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Abba Gida-Gida zai binciki Ganduje

A wani labarin, kuma kunji yadda sabon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa, zai bincike gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta kare don gano tushen wasu matsaloli

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka rantsar Abba Gida-Gida a filin wasannin Sani Abacha da ke jihar ta Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ba sabon abu bane, gwamna Abdullahi Ganduje da Abba Gida-Gida ba sa jituwa a fannin siyasa da kuma yadda alakarsu take da Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel