Sarakunan Yarbawa Sun Yi Kira Da a Dawo Da Matsayin Masarautu a Kundin Tsarin Mulki

Sarakunan Yarbawa Sun Yi Kira Da a Dawo Da Matsayin Masarautu a Kundin Tsarin Mulki

  • Sarakunan Yarbawa na neman a dawo da matsayin da sarakuna su ke da shi a baya a kundin tsarin mulkin ƙasar nan
  • Sarakunan sun bayyana cewa hakan zai kawo ci gaga sosai, da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a ƙasa gaba ɗaya
  • Sun kuma buƙaci gwamnatin Bola Tinubu mai kamawa nan da ƴan kwanaki kaɗan, da ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya

Abuja - Sarakunan Yarbawa a ƙarƙashin ƙungiyar Yoruba Obas Forum, sun yi kira da a dawo da matsayin da aka ba sarakuna a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan na shekarar 1969.

Ƙungiyar wacce ta ƙunshi manyan sarakunan Yarbawa daga yankunan Kudu maso Yamma da Arewa ta tsakiya, sun bayyana cewa hakan zai kawo zaman lafiya da daidaito a ƙasar nan, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Kulla-Kullar Dawo Da Ahmed Lawan a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10

Sarakunan Yarbawa sun yi kira a dawo da ikon masarautu
Wasu sarakunan Yarbawa tare da shugaba Buhari Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma Molokun na Atijere, Oba Samuel Adeoye, babban sakatarenta kuma Olukotun na Ikotun-Ile, Oba Abdulrasaq Abioye, da kuma Dr Michael Ajayi, suka fitar, ƙungiyar ta bayyana cewa masarautun gargajiya suna da rawar da za su taka wajen cigaban al'umma.

Sarakunan sun bayyana cewa ba su rawar da za su taka a kundin tsarin mulki, zai kawo ci gaba sosai ga mutanen da ke yankunan karkara, wanda hakan zai kawo ci gaba sosai a ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi kira na musamman ga Bola Tinubu

Sarakunan sun kuma yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya mayar da hankali wajen ganin ya kawo, tsare-tsare waɗanda za su ƙara inganta rayuwar ƴan Najeriya, cewar rahoton The Nation.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati mai kamawa ta Tinubu, da ta ware kaso 50% na kuɗaɗen tsaro ga sarakuna domin ganin sun tabbatar da tsaro a yankunan su.

Kara karanta wannan

Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi

Sun kuma yi kiran da aka sakarwa ƙananan hukumomi mara, a ƙarƙashin sa idon sarakunan gargajiya.

Shugaba Buhari Ya Ce Ministoci Su Ci Gaba Da Aiki

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya gayawa ministocinsa cewa su ci gaba da zuwa ofis har zuwa ranar ƙarshe ta wa'adin mulkinsa.

Shugaban ƙasar ya bayar da wannan umurnin ne a yayin da ya rage masa saura ƴan kwanaki kaɗan ya bar ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel