Daidai Ruwa Daidai Tsaki: Matashiya Ta Kerawa Kanta Dan Karamin Gida a Bidiyo

Daidai Ruwa Daidai Tsaki: Matashiya Ta Kerawa Kanta Dan Karamin Gida a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa mai tunani ta yi amfani da dan kudaden da take da shi wajen gina dan karamin gida a kan filinta don ta daina biyan haya
  • Da take wallafa bidiyon gidan, matashiyar ta ce koda dai gidan bai da girman sauran gidaje da aka saba gani, tana matukar farin ciki da shi
  • Masu amfani da TikTok sun garzaya sashinta na sharhi domin jinjina mata a kan wannan babban hanya da ta dauka na mallakar muhalli

Wata matashiya budurwa, @kakokaondjafa, ta wallafa bidiyon dan karamin gidan da ta ginawa kanta. Ta ce ta kasa yarda wai ita ma ta zama mai gidan kanta.

Gidan matashiyar dan karami ne kamar dai irin ginin da ake yi wa masu gadi a manyan gidaje. An shimfida tayil a kasan ginin.

Matashiya da dan karamin gidanta
Daidai Ruwa Daidai Tsaki: Matashiya Ta Kerawa Kanta Dan Karamin Gida a Bidiyo Hoto: @kakokaondjafa
Asali: TikTok

Matashiya ta cika da farin ciki kan dan karamin gidanta

A gefen ginin mai daki daya akwai wani gado da aka shirya tsaf. Yana da dan karamin wundo a gaba. Mashigi daya tilo da ake da shi na gidan na dauke da kofar katako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyon, an gano ta tana fentin cikin gidan. Ta ce fentin na kasuwanci ne ba wai don gidan ba. Kalamanta:

"...wannan na kasuwancina ne."

Da take yi wa bidiyon gininta take, ta ce:

"Na kasa yarda na gina gidana. Na san ba babba bane amma a kalla yanzu ina da makwancin da zan kira nawa."

A wani bidiyo da ta wallafa, matashiyar ta yi ikirarin cewa ta yi amfani da bulo 310 wajen ginin. Lokacin da aka isa gareta kan yadda take niyan zama a gidan tare da iyalinta, ta ce:

"Uwa mai zaman kanta da yara uku. Mun shirya ma tafiyar."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@BIG MERCY ta ce:

"A kalla ba kya biyan kudin haya hakan ya yi kyau."

@Cameroon football coach ya ce:

"Ina alfahari da ke yar'uwa. Allah ya kara daukaka amma ta yaya zan adana bidiyon."

@Stesh icequeen ta ce:

"Zan yi irin haka a malindi nagode da kika wayar mun da kai."

@incognito ta tambaya:

"Babu wajen bahaya da wajen wanka?"

@cissy321 ta ce:

"Ban san yaushe ne zan ce wannan gidana bane."

Saurayi ya gwangwaje budurwarsa da hadaddiyar mota

A wani labarin, mun ji cewa wani bidiyon TikTok da ke nuna tsantsar so da kauna na wasu masoya ya yi fice a duniyar soshiyal midiya kuma ya dauka hankalin mutane.

Bidiyon wanda ya tsuma zukatan masu kallo da kuma nuna lokacin farin ciki tsakanin masoyan, ya ja hankalin mutane da dama sannan ya sanya farin ciki a fuskokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel