“Ubangijina Dan Ruwa Ne”: Matashiya Yar Najeriya Wacce Ta Bar Addinin Kiristanci Ta Magantu

“Ubangijina Dan Ruwa Ne”: Matashiya Yar Najeriya Wacce Ta Bar Addinin Kiristanci Ta Magantu

  • Chinaza Adaigbo, wata matashiya yar Najeriya da ta dukufa wajen bautar ruwa ta bayyana cewa babu Ubangiji daya sai mahalicci guda
  • A cewar matashiyar wacce ta yi ridda daga addinin kiristanci, mahalicci gudan ya zo a nau'i daban-daban wanda daya daga ciki shine ruwa
  • Ta caccaki Nollywood, tana mai zargin masana'antar da yin fina-finan da ke bata yan ruwa da al'adun Afrika

Wata matashiya yar Najeriya, Chinaza Adaigbo, wacce ta bar addinin Kiristanci don bautar ruwa ta caccaki masana'antar Nollywood kan shafawa ruwa da al'adun Afrika bakin fenti.

Chinaza ta magantu game da abun bautarta a yayin wata hira da shahararriyar mai gabatar da shirye-shirye Lucky Udu.

Matashiya cikin ruwa
“Ubangijina Dan Ruwa Ne”: Matashiya Yar Najeriya Wacce Ta Bar Addinin Kiristanci Ta Magantu Hoto: @luckyudu
Asali: Instagram

Matashiyar wacce ta yi ridda daga addinin kiristanci ta ce yan ruwa suna da wani irin karfi na musamman wanda bai da alaka da mugunta kamar yadda mutane ke yi masu kallo.

Kara karanta wannan

Mazauna Unguwar Kurmin Kogi Sun Koka Kan Rashin Wuta Na Tsawon Shekaru 8 a Kaduna

A cewarta, ruwa kyauta ne daga Allah, tana mai raddi ga Kiristoci da Musulmai cewa idan ruwa abu mara kyau ne, da ba za su yi amfani da shi wajen tsarkake kansu yayin shiga wuraren bautansu ba. Kalamanta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na yarda cewa ruwa na da karfi na musamman saboda kyauta ne daga mahalicci. Ba shi da nasaba da mugunta kamar yadda wasu mutane ke masa kallo.
"Yanzu, da ruwa abu ne mara kyau, me yasa Kiristoci ke shiga kogi don tsarkake kai? Me yasa Musulmai ke amfani da ruwa wajen wanke kafafunsu kafin shuga wajen bautarsu? Yana nuna maka cewa ruwa na da karfi na musamman da amfani na tsarkake kai.

Chinaza ta ce Fastoci na zuwa gareta

Chinaza ta ce idan ta shiga tare da yin addu'a tana jin karin karfi tattare da ita a cikin ruwan. Sabanin yadda yake a fina-finai, ta ce ba sa sadaukar da rayukan mutane ga yan ruwa sai na dabbobi.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Sha Suka Bayan Ta Boye Fuskar Mijinta a Hotunan Shakatawa Da Suka Fita

Ta kuma tuna yadda ta ga kanta a cikin ruwa a mafarkai lokacin da take matsayin kirista, tana mai cewa fastoci na zuwa wajenta neman taimako."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@anti_odds ta ce:

"Ruwa bai da makiyi don Allah ce mata ta shiga ciki-ciki ina so na duba abu ne."

@bitcoin_chief ya ce:

"Duk abun da ya yi wa mutum idan har ba za ka cutar da wani ba bani da matsala. Turawa sun ce kiristoci su je birnin Kudus sannan su rubuta addu'o;'i kan takardu da yin addu'a a bango kuma sun yi ikirarin cewa yana aiki. Musulmai na zuwa Makka da jifan shaidan kuma yana yi masu aiki. Ni ina kira ga Amadioha magabatana kuma yana aiki. Kowa ya yi abun sa."

Rahama Sadau ta sha caccaka saboda shigar nuna tsaraici a taron AMVCA

A wani labari na daban, mun ji cewa jarumar fim, Rahama Sadau ta sha suka a wajen jama'a saboda yanayin shigar da ta yi zuwa wajen taron karrama yan fim.

Mutane da dama a soshiyal midiya na ganin shigar tata bata nuna al'ada ta mallam Bahaushe ko wacce ta fito daga yankin arewa kuma musulma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel