“Ni Cokali Ce?” Masoya Sun Yi Fice a Intanet Bayan Saurayi Ya Gwangwaje Sahibarsa Da Kyautar Mota

“Ni Cokali Ce?” Masoya Sun Yi Fice a Intanet Bayan Saurayi Ya Gwangwaje Sahibarsa Da Kyautar Mota

  • Wani attajirin matashi dan Najeriya ya tsuma zukata da dama a soshiyal midiya bayan ya gwangwaje budurwarsa da tsaleliyar mota sabuwa dal
  • Bidiyon ya nuno lokacin da ya fito da matashiyar sannan ya gabatar mata da tsadaddiyar motar
  • Jama'a sun ji dadin hakan inda suka garzaya sashin sharhi na bidiyon don bayyana ra'ayoyinsu a kan kyautar

Wani bidiyon TikTok da ke nuna tsantsar so da kauna na wasu masoya ya yi fice a duniyar soshiyal midiya kuma ya dauka hankalin mutane da dama bayan @oghalejessica ta wallafa shi.

Bidiyon wanda ya tsuma zukatan masu kallo da kuma nuna lokacin farin ciki tsakanin masoyan, ya ja hankalin mutane da dama sannan ya sanya farin ciki a fuskokinsu.

Saurayi ya yi wa budurwarsa kyautar mota
“Ni Cokali Ne?” Masoya Sun Yi Fice a Intanet Bayan Saurayi Ya Gwangwaje Sahibarsa Da Kyautar Mota Hoto: @oghalejessica.
Asali: TikTok

Saurayi ya yi wa budurwa bazata da sabuwar mota

Bidiyon ya fara ne da nuno saurayin da masoyiyarsa a cikin gida inda ya rufe mata fuska, sannan suka kama hanyar fita waje.

Kara karanta wannan

“Uba Ya Kasa Shanye Hawayensa”: Matashi Ya Fashe Da Kuka Shabe-Shabe Yayin da Diyarsa Ta Amarce

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fargabar da farin ciki ya kara karuwan yayin da suka fita waje, sannan saurayin ya nuna mata kyautar da ya yi mata na bazata.

Ya cire hannunsa daga fuskar ta, sannan sai ga sabuwar mota dal a gabanta. Ta kasa yarda da abun da idanunta suka gani kuma kyautar ya matukar burge ta.

Gaba daya fuskarta ya nuna tsantsar farin cikin da take ciki yayin da ta rungume saurayin nata cike da so kauna sannan ta nuna godiya.

Farin cikin masoyan ya burge mutane da dama kuma ya sa bidiyon ya yadu cikin sauri inda da dama suka nuna farin cikinsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@reginaene256 ta yi martani:

"Na tayaki murna, Allah ya kara budi sai yaushe ko saurayi babu."

@priscaeberechukwu1 ta ce:

"Na tayaki murna yar'uwa Allah ya yi mun irin ya taki."

Kara karanta wannan

"Yana Iya Zautar Da Mutum": Yadda Matar Aure Ta Ci Amanar Mijinta Na Sunnah, Sam Ba Ta Yi Da Na Sani Ba

@charmingsandy1:

"Allah wai ni cokali ne na tayaki murna, yar'uwa Allah ya yi mun ya taki."

@priscarichy1: '

" Na tayaki murna momma ❤️ Allah ya yi mani irin taki❤️❤️''

@brenda_enekwa2000:

"Awnn.. na tayata murna, a bangarena, da zaran ka kulle idanuna yayin da muke fita waje zan san cewa mota ka siya."

Sauyawar wasu masoya da suka dade tun basu da komai ya dauka hankali

A wani labarin kuma, wasu ma'aurata sun dauka hankalin jama'a da dama a soshiyal midiya bayan sun ci karo da hotunan sauyawar da suka yi.

Ma'auratan suna tare tun basu da komai har zuwa yanzu da Allah ya wadata su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel