Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Durfafi Coci Da Nufin Samo Miji Ko Ta Wane Irin Hali

Bidiyon Wata Budurwa Da Ta Durfafi Coci Da Nufin Samo Miji Ko Ta Wane Irin Hali

  • Wata budurwa ta ce ko ta wane irin hali ne, dole ne ta sami mijin aure da take ganin ya dace da ita
  • A cikin wani faifan bidiyo da @ninacharles8 ta wallafa, ta nuna yadda ta shiga coci, ta na mai shan alwashin samun miji
  • Bidiyon ya haifar da muhawara a tsakanin mabiyanta a kan TikTok bayan wallafa shi, kuma ya yi ta yawo a dandalin

Wata budurwa da ta ɗaura ɗamarar neman mijin aure ta kutsa kai cikin wani coci domin neman wanda zai aureta.

A cikin wani faifan bidiyo da @ninacharles8 ta wallafa, budurwar ta ɗauki bidiyon kanta a yayin da take shiga cocin.

Ta ce ta na fatan samun mijin da ya dace da ita a cocin, inda ta sha alwashin cewa babu abin da zai dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Sha Suka Bayan Ta Boye Fuskar Mijinta a Hotunan Shakatawa Da Suka Fita

Budurwa ta ce dole ne ta samu miji ko ta wane hali
Budurwa ta je coci da nufin samo miji ko ta wane hali. Hoto: @ninacharles8
Asali: TikTok

Ta ce dole ne ta samu miji ko ta wane hali

A cewarta, dole ne ta samowa kanta miji a cikin cocin, koda ta karfi da yaji ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta yi wa cocin tsinke da azama a muryarta a yayin da kuma ta ke bayyanawa mabiyanta na TikTok manufarta cikin ɗaga murya.

Ta ce shugabannin addini sun fuskanci barazana a baya, sai da suka sa karfi sannan suka iya tabbatuwa, don haka ita ma za ta yi amfani da ƙarfin wajen neman mijin nata.

Bidiyon dai gwanin ban dariya ya jawo muhawara a tsakanin mabiyanta.

Kalli bidiyon a kasa:

Tsokaci daga masu amfani da TikTok yayin da wata budurwa ta durfafi coci domin neman mijin aure

@user9471732153921 prince ya ce:

"kwantar da hankalin ki, ga ni nan."

@dasmithcomedy ya ce:

"Abinda kawai ya rage shi ne ki sanya sayimbol a gefen titi na neman mijin."

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

@Fatokun Osuolale Olanrewaju ya ce:

"Sarauniyar zuciya."

@babs Kuffay said:

"Ubangiji ya cika miki burin zuciyarki. Amin."

@Johnson Ibe ya ce:

"Yi ƙoƙarin nemo mijin aure, ina miki fatan alkhairi."

@King David ya ce:

"Da wasa kike? ta yaya hakan ta faru?"

@Patience Wilson Isong ta ce:

"Da ƙarfi da yaji? tsohuwa 'yar shekara 70."

Wata budurwa ta maka mahaifinta kotu kan auren dole

A wani labarin na daban, wata budurwa a Kaduna ta kai ƙarar mahaifinta gaban kotun Musulunci kan yunƙurin yi ma ta auren dole.

Budurwar mai suna Fatima, ta nemi kotun ta hana mahaifin na ta aurar da ita ga wani mutumin da ta bayyana cewa ba ta so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel