“Ina Kansa Yake?” Matashiya Ta Sha Caccaka Kan Wallafa Hotunan Rabin Jikin Mijinta

“Ina Kansa Yake?” Matashiya Ta Sha Caccaka Kan Wallafa Hotunan Rabin Jikin Mijinta

  • Yunkurin wata mata na nunawa duniya sahibin ranta ya gamu da tangarda yayin da masu amfani da soshiyal midiya suka caccaketa saboda hoton mijin nata
  • Hakan ya kasance ne saboda sai da ta tabbatar ta yanke fuskar mijin a dukkanin hotunan da ta saki, yayin da ta bar tata fuskar
  • Mutane da dama sun cika da al'ajabin dalilin da zai sa ta aikata haka ga mutumin da suka yi ikirarin shine ya dauki nauyin tafiyar, wasu na son sanin me yasa ta wallafa rabin hotuna

Wallafar da wata matashiya ta yi a twitter ya haddasa cece kuce a soshiyal midiya bayan ta saki hotunan mijinta ba tare da fuska ba a dandanlin.

@ParisNotFrance_ ta wallafa hotuna uku daga yawon shakatawar da suka je da mijinta amma sam abun bai yi wa jama'a dadi ba.

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

Masoya a wajen yawon shakatawa
“Ina Kansa Yake?” Matashiya Ta Sha Caccaka Kan Wallafa Hotunan Rabin Jikin Mijinta Hoto: @ParisNotFrance_.
Asali: Twitter

Mutane sun caccake ta kan boye fuskar mijin nata a gaba daya hotunan, domin hakan ya sa sun gaza sanin wanene shi ko yaya kamanninsa yake.

Wasu kuma sun yi hasashen cewa lallai tana cin amana ne tun da har ta aikata haka, yayin da wasu suka fadi albarkacin bakunansu tare da yi mata wankin babban bargo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba tare da nuna damuwar komai ba, matashiyar ta kara bayyanawa a sashin sharhi cewa amininta take aure. Wallafarta ya samu 'likes' 13k a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Jama'a sun yi martani

@Randomu02934236 ya ce:

"Ba ki ma saka emoji ba a kan mijin, kawai yanke shi kika yi, duniya ce mai sanyi."

@SheFell4Russia ya ce:

"Dan uwa ya kashe tattalin arzikinsa amma duk da aka sai da aka yanke kansa wannan mugun wasa ne."

Kara karanta wannan

Likitocinmu na gobe: Yadda dalibin likitanci ke tikar rawa bayn rubuta jarrabawar karshe ya jawo cece-kuce

@drewjerseey ta ce:

"Tambaya ta gaskiya, idan kuka aikata haka shin saboda ba ku son a gane mijinku ne idan yana cin amana sannan a zo a fada maku? ko kuma kuna yin haka ne don ba ku son mutane su ga wanda kuke soyayya da shi a yanzu ne saboda wani dalili?"

Yanayin shigar Rahama Sadau zuwa bikin karrama yan fim ya bar baya da kura

A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a da dama a soshiyal midiya sun caccaki jarumar Kannywood, Rahama Sadau saboda yanayin tufafin da ta sanya zuwa wajen taron karrama yan fim da ya gudana a jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel