Yanayin Shigar Rahama Sadau Zuwa Wajen Wani Taro Ya Bar Baya Da Kura

Yanayin Shigar Rahama Sadau Zuwa Wajen Wani Taro Ya Bar Baya Da Kura

  • Fitacciyar jarumar kannywood, Rahama Sadau, ta yi shiga ta kece raini zuwa wajen taron karrama yan fim na 2023
  • Jama'a sun caccaki jarumar ta Kannywood saboda yanayin shigarta cewa sam bai dace da yar arewa kuma musulma ba
  • Darakta Abubakar Bashir Maishadda ya samu lambar yabo a taron kuma masoya sun taya shi murnar wannan nasara

A ranar Asabar, 20 ga watan Mayu ne aka gudanar da bikin karrama yan fim na African Magic Viewers Choice Awards (AMVCA) a jihar Lagas.

A masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood gaba daya, Abubakar Bashir Maishadda ne kadai ya samu lambar yabo na ‘best indigineous Language Hausa’ da fim dinsa mai suna 'Aisha'.

Daraktan ya wallafa hotunan taron a shafinsa na instagram inda ya kara godewa Allah a kan zabarsa da ya yi cikin dubban jama'a.

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

Sai kuma Rahama Sadau wacce an zabe ta amma bata samu damar karbar lambar yabo ba amma ta yi jawabi a wajen.

Bashir Maishadda da Rahama Sadau
Yanayin Shigar Rahama Sadau Zuwa Wajen Wani Taro Ya Bar Baya Da Kura Hoto: realabmaishadda
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da Maishadda ya burge mutane da dama saboda yanayin shigarsa da kuma yadda ya jaddada godiyarsa ga Allah cikin harshensa ta Hausa abun ya sha banban a bangaren Rahama Sadau.

Yanayin kayan da Rahama ta sanya zuwa wajen taron ya dauka hankalin jama’a sosai a soshiyal midiya inda suka dungi tofa albarkacin bakunansu.

Mutane da dama na ganin sam shigar jarumar bai dace ba ko kadan musamman duba ga cewar taro ne na nuna al’adu.

Jarumar dai ta sanya matsatsiyar doguwar riga ta zamani sannan ta yi karin gashi kuma ta bar kan nata a bude ba tare da ta yane shi da dankwali ba.

Mutane da dama sun kushe wannan shiga ta Rahama inda wasu suka ce sam basu gane ita bace ma da farko saboda ko kadan bata wakilci yankin arewacin kasar ba.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Abun da mutane ke fadi game da shigar Rahama Sadau

yarblessings ta yi martani:

Allah yasa albarka, wai Rahma Sadau tana tunanin wannan shashancin da take zata wanye lafia? Gaskia abinda kike bakya kyautawa kanki kuma kinci amanar musulunci wlh Allah bazai barki ba, idan kinfi karfin iyayenki saboda kina hada halak da haram ay bakifi karfin Allah ba. Allah yasamu a hanyar tafarki madaidaici, Ya Allah duk kudi da daukakar da zamu samu kuma mu kauce maka Allah karka bamu So annoying wlh."

dangibagudu ya ce:

"Wai Dan Allah iyayen rahamasadau na nan da ransu???"

muhdahmad72 ya ce:

"Nayi Allah wadai da shigar da Sadau tayi ."

dabogi_collections ta ce:

"Idan mutum ya fadi ya mutu a haka dawani baki zaice ma Allah imaninshi a zuciya yake....Ga wanda ya shafa Allah ya shirya mana zuria.... Ina tayaka murna darakta Allah ya Kara daukaka."

dk_exclusive_scents ta ce:

"Bakin mutane kadai ya isheki sadau,kai kuma ina tayaka murna Allah ya kara daukaka amma dan Allah kuna mata nasiha,rayuwar nawa take,vanity cefa ."

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

khabeer__mudallib ya ce:

"Kaga wata shiga da tayi Allah wadaran naka ya lalace Allah ka shiryemu baki daya Allah kasa mudace Amman indai wannan ce wayewa to wlh Allah waye war nan batai baAllah kasa mudace @rahamasadau ‍♀️."

Yar shekaru 53 ta shiga daga ciki bayan shafe shekaru tana jiran tsammani

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata mata yar Najeriya mai shekaru 53 ta amarce da sahibinta mazaunin Amurka bayan ta shafe shekaru masu yawa tana jiran tsammani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel