Tsananin Kishi Ya Sanya Matar Aure Yunkurin Halaka Diyar Makwabcinta a Jihar Kano

Tsananin Kishi Ya Sanya Matar Aure Yunkurin Halaka Diyar Makwabcinta a Jihar Kano

  • Wata matar aure ta yi yunƙurin halaka wata ƙaramar yarinya mai shekara shida a duniya a jihar Kano
  • Matar auren mai suna Fatima Malam, ta yi yunƙurin halaka yarinyar saboda mahaifinta ya ba mijinta shawarar ya yi mata kishiya
  • Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce suna ƙoƙarin cafko matar auren wacce ta gudu

Jihar Kano - Wata ƙaramar yarinya mai shekara shida a duniya, Sherifat Usman, na can rai a hannun Allah, bayan wata mata mai suna, Fatima Malam, ta caccaka mata wuƙa a cikinta a jihar Kano.

The Punch ta kawo rahoto cewa Fatima ta cakawa yarinyar wuƙa domin nuna ɓacin ranta kan shawarar da mahaifinta, ya ke ba mijinta na ya yi mata kishiya.

Matar aure ta yi yunkurin halaka ƙaramar yarinya a Kano
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Gumel Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun bayyana cewa Fatima ta ji haushi ne bayan ta gano cewa mahaifin Sherifat, wanda abokin mijinta ne, shine ya ke ba shi shawara ya ƙaro aure.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Kuskure: An Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

Sai dai, mijin Fatima mai suna Malam, ya yi iƙirarin cewa matarsa na da taɓin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkansu dai suna rayuwa ne a Gadon Kaya Damatsiri a cikin ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Majiyoyin sun bayyana cewa Fatima ta nemi Sherifat da ta rakata zuwa unguwar Mariri cikin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda a nan ne ta aikata mata wannan ɗanyen aikin.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa:

"Akan hanyarsu ta zuwa Mariri, Fatima ta siyo wuƙa bashi. Ta kai Sherifat cikin wani kango inda a nan ne ta caccaka mata wuƙa a ciki da niyyar halaka ta."

Bayan ta aikata wannan ɗanyen aikin Fatima ta yi gaggawar sulalewa daga wajen, inda ta yi tunanin cewa yarinyar ta sheƙa barzahu.

Sai dai, kukan da yarinyar ta ke yi ne, ya janyo hankalin mutanen da ke wucewa ta wajen, inda suka samu suka ceto ta.

Kara karanta wannan

"Za Mu Sake Dawowa": Gwamna Ganduje Ya Sha Muhimmin Alwashi Ga Kanawa

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a ranar Laraba.

Sai dai, ya bayyana cewa har yanzu ana cigaba da bincike kan lamarin, yayin da ƴan sanda ke ƙoƙarin cafke matar wacce ta cika bujenta da iska.

Motar Kamfanin Dangote Ta Murkushe Wani Dan Sanda Da Wasu Mutane 3 Har Lahira

A wani labarin na daban kuma, wani hatsarin mota ya ritsa da motar kamfanin Dangote a jihar Ogun, inda mutane da dama suka riga mu gidan gaskiya.

Haɗarin motar wanda ya auku akan hanyar Abeokuta zuwa Legas, ya yi sanadiyyar rasa ran wani ɗan sanda da wasu mutum uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel