Subhanallahi: Wata Mata Ta Rasa Ranta a Kokarin Raba 'Ya'yanta Fada a Birnin Tarayya Abuja

Subhanallahi: Wata Mata Ta Rasa Ranta a Kokarin Raba 'Ya'yanta Fada a Birnin Tarayya Abuja

  • Wata mata ta gamu da ajalinta lokacin da ta yi ƙoƙarin shiga tsakani ta raba ƴaƴanta masu faɗa a birnin tarayya Abuja
  • Ɗaya ɗaga cikin yaran ne dai ya kantara mata sara da adda bisa kuskure, inda ɗmdaga ƙarshe tace ga garin ku nan
  • Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace tana cigaba da gudanar da bincike

FCT Abuja - Wata mata mai suna Zainab Ibrahim ta gamu da ajalinta, yayin da ta je rabon faɗan da ya ɓarke a tsakanin ƴaƴanta biyu, masu suna Inusa da Usman.

The Punch tace duk da dai ba a san maƙasuɗin faɗan yaran ba, Inusa ya sari mahaifiyarsa da adda a hannun hagu bisa kuskure.

Wata mata ta rasa ranta wajen raba 'ya'yanta fada a Abuja
Kakakin rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh Hoto: @Jossy_Dannyking
Asali: Twitter

Lamarin ya auku ne ranar Asabar a yankin Kpaduma II a Asokoro cikin birnin tarayya Abuja, cewar rahoton Daily Post.

Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana sunan shi a matsayin, Saliu Shehu, yace an garzaya da Zainab wani asibitin kuɗi, inda ta ce ga garin ku nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Yaran ƴan'uwan juna ne iyayensu ɗaya. Mummunan faɗa suke yi a tsakaninsu, sai mahaifiyarsu ta zo ta yi ƙoƙarin raba su. Sai dai, Inusa ya tafi ya ɗauko adda wacce ya yi niyyar amfani da ita kan ɗan'uwansa."
"A garin hakan ne, ya sari mahaifiyarsa a hannun hagu bisa kuskure. An kai ta wani asibitin kuɗi, inda anan ta rasu."

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Ko da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta bayyana cewa Inusa ya ranta ana kare, inda ta ƙara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

A kalamanta:

"Mun samu kiran gaggawa inda ba mu yi wata-wata ba mu ka garzaya wurin da lamarin ya auku. An kai mahaifiyar asibiti, inda rai ya yi halinsa a can. Usman yana tsare a hannun mu, yayin da Inusa ya ranta a na kare. Sai dai, a na cigaba da gudanar da bincike kan lamarin."

Bam Ya Fashe a Birnin Jalingo

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wani abin fashewa ya tashi a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Abin fashewar wanda ake kyautata zaton bam ne, ya fashe ne a wata mashaya cikin birnin, inda ya raunata mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel