Wani Bam Ya Tashi a Wata Mashaya a Birnin Jalingo Na Jihar Taraba

Wani Bam Ya Tashi a Wata Mashaya a Birnin Jalingo Na Jihar Taraba

  • Mutane a birnin Jalingo na jihar Taraba sun shiga firgici, bayan wani abin fashewa ya fashe a birnin
  • Abin fashewar wanda ake kyautata zaton bam ne ya fashe ne dai a wata matsaya da ke cikin birnin na Jalingo
  • Ba a samu asarar rayuka ba, amma mutane da dama sun samun raunika, inda aka garzaya da su zuwa asibiti

Jihar Taraba - Wani abin fashewa wanda ake kyautata zaton bam ne, ya fashe a daren ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a wajen wata mashaya a Doruwa kusa da bankin Polaris, sannan ya shafi wasu gine-gine a yankin, yayin da mutane da dama waɗanda ba a san yawansu ba, suka samu raunika.

Bam ya tashi a birnin Jalingo na jihar Taraba
Taswirar jihar Taraba Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Channels Tv ta yi rahoto cewa wata budurwa ta samu mummunan rauni, inda aka garzaya da ita wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Ba a samu asarar rai ba a tashin bam ɗin, sai dai mutane da dama da suka samu raunika a dalilin fashewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni jami'an ƴan sanda masu hana tashin bam suka zagaye wajen domin hana aukuwar tashin wani bam ɗin, idan har ta yiwu an dasa wani bam ɗin a kusa da wajen.

Tashin bam ɗin da ya auku a Doruwa, shine na huɗu da ya taɓa aukuwa a babban birnin jihar tun shekarar 2022, sannan na biyar da ya auku a jihar tun shekarar 2022.

Gwamnatin jihar Taraba da jami'an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba, dangane da wannan lamarin har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Jalingo mai suna Hassan Kundi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

"Ka yi hauka ne?": Tashin hankali yayin da mawaki ya kaftawa dan sandan Najeriya mari

Hassan ya bayyana cewa tsakanin su da unguwar da lamarin ya auku babu wani nisa sosai, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:40 na daren ranar Lahadi, a mashayar da ke a Doruwa.

Ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a wajen amma dai mutane da dama sun jikkata.

Bam Ya Tashi Da Shugaban Masu Hada Bam Na 'Yan Ta'addan Boko Haram

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa bam ya tashi da wani babban shugaban masu haɗa bam na ƙungiyar ta'addancin Boko Haram.

Bam ɗin ya tashi ne da Awana Gaidam, wanda shine shugaban masu haɗa bam na ƙungiyar, cikin dajin Sambisa.

Gaidam dai ya dasa bam ɗin ne domin ya tashi da dakarun sojoji, sai kuma dara ta ci gida, inda bam ɗin ya tashi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel