"Budurwa Daya Matsala": Matashi Mai Soyayya Da 'Yanmata Biyu Ya Nuna Su, Bidiyon Ya Dauki Hankula

"Budurwa Daya Matsala": Matashi Mai Soyayya Da 'Yanmata Biyu Ya Nuna Su, Bidiyon Ya Dauki Hankula

  • Wani matashi ɗan Najeriya mai soyayya da ƴanmata biyu a tare, ya nuna wa duniya su a soshiyal midiya
  • Matashin ya yi wa masu budurwa ɗaya shaguɓe, inda ya ke cewa lallai ana ci da rabonsu da su ke yin soyayya da mace ɗaya
  • Matashin ya kuma yi magana kan shirin aurensu da ya ke inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikinsu tana da kishi

Wani matashi ɗan Najeriya mai suna, @innowire__1, ya janyo cece-kuce a yanar gizo, bayan ya nuna ƴanmata guda biyu da ya ke soyayya da su.

A cewar matashin, yana ƙaunarsu su duka biyun, kuma yana da shirin yin wuff da su a lokaci guda.

Matashi ya nuna kyawawan 'yanmatan da ya ke soyayya da su
Matashin ya ce a tare zai yi wuff da su Hoto: @innowire_1
Asali: TikTok

A shafinsa na TikTok, matashin ya cigaba da bayani kan yadda soyayyarsa ta ke gudana tsakaninsa da ƴanmatan biyu.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yan Uwan Juna Sun Baiwa Hammata Iska Kan Kuɗin Sadaƙin Yar Uwarsu N250,000

A ɗaya daga cikin wallafar da ya yi, ya bayyana cewa ɗaya daga cikinsu ƴar ƙasar Ghana ce, sannan wacce ake kira da Loveth a cikinsu tana da tsananin kishi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi wa masu soyayya da budurwa ɗaya shaguɓe, inda ya ce garaɓasa ta bar su.

A cikin wani bidiyo wanda ya nuna ƴanmatan na sa, matashin ya bayyana cewa akwai ƙura yin ƴanmata biyu.

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

angel ta rubuta:

"Ɗan rainin wayau, ko kunya baka ji za ka auri mata biyu."

Joy Chioma ta rubuta:

"Ina ɗayar ta ke kallo ne nan za ki kallo ai."

Loveth Akogwu ta rubuta:

"Amma ina ganin sun ɗan yi kama kaɗan fa."

user3156094070716 ya rubuta:

"Kuma kamar su duka juna biyu garesu, waaah father bernard ƙara daurewa dai, ba sauƙi."

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis

That_RICH__MF ya rubuta:

"Wannan fuskar ta yi Ghana amma tana India."

Blessing12 ta rubuta:

"Kai mutumina ba ka da dama ooooh."

annogamba ya rubuta:

"Amma a cikin su biyun wacce za ka aura, ban zo da rigima ba."

Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Za ta Koma Kasarsu

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka da soyayyar nesa bayan budurwarsa baturiya za ta koma ƙasarsu.

Matashin dai kamar wani ƙaramin yaro ya yi ta sharɓar kuka, inda ya ce zai yi kewar masoyiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel