'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Imo

'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Imo

  • Ƴan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na ƙauyen Umuarugo cikin jihar Imo
  • Hon. Chinedu Eleliam ya faɗa hannun ƴan bindiga ne bayan sun biyo shi har gida sannan suka yi awon gaba da shi
  • Har ya zuwa yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalan Chinedu ba, domin sanin halin da ya ke ciki, wanda hakan ya sanya tsoro a zukatan mutanen ƙauyen

Jihar Imo - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Hon. Chinedu Eleliam, na ƙauyen Umuarugo a mazaɓar Umueze ll, cikin ƙaramar hukumar Ehime Mbaino, a jihar Imo.

Leadership ta rahoto cewa ƴan bindigan waɗanda ake zargin makiyaya ne, sun biyo sawunsa ne har gida a wasu motoci biyu, inda daga nan suka yi ta harba bindigu domin firgita mutane.

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis

'Yan bindiga sun sace shugaban APC a jihar Imo
Taswirar.jihar Imo Hoto: 247ureports.com
Asali: UGC

Wani majiya a ƙauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan bindigan sun kamo Eleliam ne sannan suka tura shi cikin motar su da ƙarfin tsiya, inda daga nan suka ranta a na kare ana tsaka da harbe-harben bindiga.

A cewar majiyar, tsoro ya mamaye zukatan mutanen ƙauyen, domin har ya zuwa yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalansa ba, cewar rahoton The Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sace shugaban jam'iyyar dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga, sun halaka tsohon kyaftin ɗin soja, Tony Enoch, na hannun daman gwamna Hope Uzodinma, wanda shine shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ƙaramar hukumar Oru-East.

Ƴan sanda sun fara gudanar da bincike

Tuni rundunar ƴan sandan jihar, ta fara farautar ƴan bindigan da ke da hannu a kisan Enoch.

Kakakin rundunar Henry Okoye, ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Ahmed Barde, ya bayar da umurnin gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike domin cafke miyagun da suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

Ekweremadu Da Sauran Jerin Manyan 'Yan Siyasar Da Aka Taba Kullewa a Kasar Waje

Yan Ta'adda Sun Sake Halaka Mutane Bakwai A Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, miyagun ƴan bindiga sun sake halaka mutum bakwai a jihar Kaduna, a wani mummunan hari da suka kai.

Ƴan bindigan sun koma lalata dukiyoyin miliyoyin naira a lokacin da suka kai harin, sannan sun raunata mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel