Ekweremadu Da Sauran Jerin Manyan 'Yan Siyasar Da Aka Taba Kullewa a Kasar Waje

Ekweremadu Da Sauran Jerin Manyan 'Yan Siyasar Da Aka Taba Kullewa a Kasar Waje

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ba shine babban ɗan siyasa na farko ba, da aka tura gidan gyaran hali a ƙasar waje
  • James Ibori, gwamnan jihar Delta daga 1999 zuwa 2007, a shekarar 2012 an tura shi gidan yari har na shekara 13 bisa cin kuɗin haram a UK
  • Wata kotu a ƙasar Amurka ta tura Abidemi Rufai, dakataccen hadimin gwamnan jihar Ogun, gidan yari har na shekara biyar bisa aikata damfara

Abuja - Hukuncin da kotu ta yanke kan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ikweremadu a UK, a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, ya sanya ƴan Najeriya tafka muhawara sosai a soshiyal midiya

Bayan kusan kwashe wata 11 yana fuskantar tuhuma kan safarar sassan jikin ɗan adam, kotu ta tura Ike Ekweremadu, matarsa mai suna Beatrice da wani likita mai suna Obinna Obeta, gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Ekweremadu da sauran 'yan siyasar da aka kulle a kasar waje
Bayan Ekweremadu akwai wasu manyan 'yan siyasa da aka taba kullewa a kasar waje Hoto: Asiwaju project beyond 2023, Ike Ikweremadu, Abidemi Rufai
Asali: Facebook

Legit.ng ta rahoto cewa Sanatan ba shi ne na farko ba a cikin manyan ƴan siyasan da aka taɓa turawa gidan gyaran hali, a ƙasar waje.

Ga jerin su kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Ike Ekweremadu

Ekweremadu, mai shekara 60 a duniya, ɗan asalin jihar Enugu ne. Sannan har zuwa lokacin da aka yanke masa hukunci, Sanata ne a majalisar dattawa. Ya kasance a majalisar dattawa tun 3 ga watan Yuni, 2003.

Mamba a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ekweremadu ya taɓa riƙe matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa. Sannan ya kuma taɓa riƙe kujerar shugaban ƙaramar hukumar Aninri a jihar Enugu.

2. James Ibori

Ibori shine kusan sunan wanda ya ke fara zuwa da an yi maganar wani ɗan siyasar da aka taɓa kullewa a ƙasar waje.

Tsohon gwamnan jihar Delta, muƙamin da ya riƙe tun daga shekarar 1999 har zuwa 29 ga watan Mayu 2007, Ibori an yanke masa hukuncin shekara 13 a gidan kaso bisa zargin cin kuɗin haram, a ranar Talata, 17 ga watan Afirilu 2012.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Kotun a lokacin shari'ar, ta kuma ƙwace kadarorin Ibori, waɗanda sun kai kimanin £17m ($35 million), a farkon watan Agustan 2007.

3. Abidemi Rufai

Abidemi Rufai tsohon hadimin gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ne.

Ya amsa yin amfani da sunayen bogi wajen damfarar shirye-shiryen rage raɗaɗin annoba na ƙasar Amurka, waɗanda suka haɗa da aid for Hurricanes Harvey and Irma, da file fraudulent U.S. tax returns.

Hukumomi a ƙasar Amurka, sun ce Rufai ya yi amfani da sunayen bogi kusan dubu ashirin, wajen tafka damfara.

Rufai wanda a lokacin ya ke da shekara 45 a duniya, an dai yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan kaso.

Tsaffin Hotunan Ekeremadu Tare Da Sarki Charles III Ya Janyo Muhawara A Intanet

A wani labarin na daban kuma, wasu tsaffin hotunan Sanata Ike Ikweremadu da sabon sarkin Burtaniya, Sarki Charles III sun janyo muhawara a yanar gizo.

Hotunan sun bayyana ne jim kaɗan bayan an yankewa Ekweremadu hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel