Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

  • Rundunar ƴan sandan jihar Edo, ta samu nasarar cafke wasu jami'an tsaro ma su aikata fashi da makami
  • Ɓata garin jami'an tsaron su biyu, an cafke su ne bisa zargin aikata laifin fashi da makami da ƙwacen mota
  • Waɗanda ake zargin dai ɗaya daga cikin su jami'in sojan ruwa ne, yayin da ɗayan kuma jami'in gandiroba ne

Jihar Edo - Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta cafke wani jami'an sojan ruwa mai suna Ibrahim Adamu, mai shekara 25 a duniya da wani jami'in gandiroba mai suna Abdullahi Abdulwahab, mai shekara 26, bisa zargin fashi da makami.

The Punch ta kawo rahoto cewa a na zargin jami'an guda biyu ne da aikata laifin fashi da makami da ƙwacen mota.

'Yan sanda sun cafke jami'an tsaro masu fashi da makami
An cafke jami'an tsaron ne sanye da kayan sojoji Hoto: Lindaikejiblog.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, yayin taso ƙeyar waɗanda ake zargin a ranar Talata, ya bayyana cewa jami'an su ne suka cafke su ne sanye da kayan sojoji a Ekpoma, biyo bayan samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Mutane Da Dama Sun Kwanta Dama Bayan Shan Shayi a Wajen Daurin Aure a Kano

Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun farmaki direban motar ƙirar C300 Mercedes Benz wacce ba ta da rajista a Sapele, cikin jihar Delta, suka ƙwace motar daga hannun sa sannan suka tilasta masa tura mu su N400,000 a cikin asusun bankin su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin suna shirin tafiya da motar ne birnin tarayya Abuja, lokacin da ƴan sanda suka cafke su a Ekpoma, cikin jihar Edo, cewar rahoton Vanguard.

Kakakin ya kuma ƙara da cewa:

"Waɗanda ake zargin sun bayar da bayanai inda suka yi iƙirarin cewa su jami'an sojin ruwa ne da gandiroba."

Nwabuzor ya ce an kwato motar da kayan sojojin da su ke a hannun waɗanda ake zargin.

Da ya ke magana da manema labarau, labarai, Ibrahim Adamu, wanda ya shiga aikin soja a shekarar 2019, ya ce an cafke shi ne bisa satar mota ƙirar Mercedes Benz C300 a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mutane 40 Sun Nutse a Wani Hadarin Jirgin Ruwa a Arewacin Najeriya

A na sa ɓangaren, Abdulwahab, jami'in gandiroba a jihar Kaduna, ya ce Adamu ne ya gayyacw shi zuwa Warri domin yin fashin, inda ya ke cewa wannan shi ne karon sa na farko da ya yi fashi da makami.

Jami’an ’Yan Sanda Sun Sheke Wasu ’Yan Bindiga Har Lahira

A wani labarin na daban kuma, jami'an ƴan sanda sun samu nasarar halaka wasu ƴan bindiga mutum biyu a jihar Anambra.

Ƴan bindigan sun gamu da ajalin su ne dai a ranar Litinin, 8 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel