Mutane Da Dama Sun Kwanta Dama Bayan Shan Shayi a Wajen Biki a Kano

Mutane Da Dama Sun Kwanta Dama Bayan Shan Shayi a Wajen Biki a Kano

  • Aƙalla mutum bakwai ne suka gamu da ajalin su, bayan shan wani shayi a wajen wani ɗaurin aure a Kano
  • Shayin an tabbatar an sanya masa zaƙami tare da wasu ƙwayoyin shaye-shaye fiye da ƙima
  • Da dama daga cikin waɗanda suka kurɓi shayin, na can kwance a asibiti rai a hannun Allah

Jihar Kano - Mutum 7 sun riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti, bayan sun sha wani shayi da ake zargin an haɗa shi da Zaƙami, a wajen wani taron ɗaurin aure a Kano.

Jaridar Daily Trust tace shaidun ganau ba jiyau ba, sun ce lamarin ya shafi kusan mutum 50, inda har yanzu ba a san inda wasu daga ciki su ke ba. Lamarin ya auku ne a Sheka cikin ƙaramar hukumar Kumbotso a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

Mutum 7 sun mutu bayan shan shayi wajen biki a Kano
Hoton wani mai sana'ar shayi, ba inda lamarin ya auku ba Hoto: Dailystar.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin shaidun mai suna, Sanusi Yahaya, wanda yaya ne a wajen amaryar, ya ce ana zargin an haɗa shayin ne da ƙwayoyi daban-daban bayan zaƙamin.

Ya bayyana cewa ya zama al'ada ga matasan yankin, musamman masu shaye-shaye su dafa shayi lokacin biki, inda suke fakewa da hakan su sha ƙwayoyi, cewar rahoton Naija Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun dafa shayin sannan su kan su ba su san ko ƙwayoyi nawa ba ne a ciki, wanda har ya kai ga wasu daga ciki sun fasa sha. Amma wasu daga ciki sun nace sai sun sha shayin, inda suke cewa ƙwaƙwalwarsu za ta iya ɗaukewa."
"Bayan shan shayin, mutum 2 sun rasu, wasu sun warke yayin da wasu na can kwance a asibiti," A cewarsa

Wani shaidar mai suna, Abdullahi Muhammad, ya ce ya zuwa ranar Talata, mutum 7 sun rasu.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda aka kwantar a asibiti, ba a yankin su ke ba, hanya ce ta biyo da su, suka ce bari su ɗan kurɓi shayin.

"Ya zuwa yanzu ba mu san adadin yawan waɗanda suka rasu ba, amma da safe an tabbatar da rasuwar mutum 7. Wasu daga ciki ko gayyatar su ba a yi ba zuwa wajen ɗaurin auren, sun yi basaja ne kawai su sha ƙwayoyin su," A cewarsa.

Ba a samu jin ta bakin angon ba, domin shi da wasu, sun ran ta ana kare.

Mutane 40 Sun Nutse a Wani Hadarin Jirgin Ruwa a Jihar Sokoto

A wani labarin na daban kuma, ƙimanin ƴan mata 40 ne suka nutse cikin ruwa a wani haɗarin jirgin kwale-kwale a jihar Sokoto.

Ƴan matan dai sun nutse ne a cikin ruwan bayan jirgin kwale-kwalen da ke ɗauke da su, ya kife.

Asali: Legit.ng

Online view pixel