Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'ya da Jikokin Sarkin Kagarko a Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'ya da Jikokin Sarkin Kagarko a Jihar Kaduna

  • Yan bindiga sun shiga har fadar mai martaba sarkin Kagarko, sun sace ya'yansa da jikoki a kudancin jihar Kaduna
  • Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kuma shiga wasu kauyuka sun tafka ta'adi kafin su koma inda suka fito
  • Kakakin rundunar yan sandan Kaduna bai ɗaga kiran waya ba yayin da aka tuntube shi don jin ta bakin hukuma

Kaduna - Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan fashin daji ne sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Kagarko a kudancin Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar.

Rahoton Daily Trust ya ce yan bindigan sun kutsa kai cikin fadar Sarkin kana suka yi awon gaba da 9 daga cikin 'ya'ya da jikokin Sarkin, da wasu mutum uku.

Kaduna.
Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'ya da Jikokin Sarkin Kagarko a Jihar Kaduna Hoto: channelstv
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya bayanansa ya ce 'yan bindiga sun shiga garin da misalin ƙarfe 11:15 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan Sarki.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

"Sun yi awon gaba da Amaryarsa, 'ya'ya da jikoki 9 amma amaryan ta gudo daga hannunsu ta koma gida," inji mutumin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa 'yan bindigan sun kuma sace wasu mutane 3 a garin Kagarko, ciki harda mace ɗaya kuma sun raunata mutum ɗaya, Audu Kwakulu a Ungwan Pah, yanzu haka yana kwance a Asibiti.

Ya ce:

"Yan bindigan jejin sun kashe Makiyayi ɗaya a ƙauyen Kuchimi, sun fasa shaguna 7 suka kwashi kaya a kauyen Janjala (Duk a karamar hukumar Kagarko) a hanyarsu ta komawa."

Wane matakin rundunar yan sanda ta ɗauka?

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kaduna, DSP Muhammed Jalige, bai ɗaga kiran wayan da aka masa ba har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton.

Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin shiyyar arewa ta yamma da ke fama da kalubalen rashin tsaro a ƙasar nan, rahoton Pulse ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara a Arewa: An Kashe Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Addabi Al'umma

Yan bindiga ko ace yan fashin jeji sun hana mutane zaman lafiya a sassan jihar duk da gwamnati ta maimaita ɗaukar alkawarin dawo da zaman lafiya a lokuta da dama.

An Kashe Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Al'umma

A wani labarin kuma Dakarun Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

Jami'an rundunar yan sanda sun yi nasarar sheƙe hatsabibin ɗan bindiga a kauyen Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

A cewar kakakin yan sanda, bayan kashe ɗan bindigan, jami'ai sun kwato Babur ɗin da suke aiki da shi, CP ya yaba da wannan nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel