Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

  • Wasu ‘yan bindiga a Kaduna sun durfafi fadar Sarkin Kagargo inda suka sace iyalinsa da wasu mazauna garin guda 3
  • ‘Yan bindigan har ila yau kuma sun raunata wani matashi, mai suna Audu Kwakulu da ke jinya yanzu haka a asibiti
  • Dadi da kari, masu garkuwa da mutanen sun fasa shaguna da dama a kauyen Kwucimi yayin da suke shirin ficewa daga kauyen

Jihar Kaduna – Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan Sarkin Kagarko a Kaduna ta Kudu, Alhaji Sa’ad Abubakar inda suka kwashe ‘ya’yansa guda 9 da jikokinsa bayan da suka kutsa cikin fadarsa.

Wani mazaunin yanki wanda ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust, ya ce ‘yan bindigan sun durfafi fadar Sarkin ne da misalin karfe 11:15 na dare.

Kaduna
Jihar Kaduna, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Bayan haka, ‘yan bindigan sun kuma yi awun gaba da wasu mazauna garin mutum 3 yayin kai harin, kamar yadda rahotanni suka tattaro.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Fadar Sarki a Kaduna, Sun Sace 'Ya'Yansa da Jikoki

“Yan bindigan sun yi garkuwa da karamar matarsa, ‘ya’ya tara da kuma jikokinsa amma matar ta kubuce daga hannun ‘yan bindigan har ta dawo gida”, in ji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa masu garkuwan sun sace wasu mutane 3, da ya hada da wata budurwa sannan suka raunata wani matashi mai suna Audu Kwakulu da ke jinya yanzu haka a asibiti.

Mazaunin yankin ya kara da cewa:

“Yan bindigan har ila yau sun kashe makiyayi guda 1 a kauyen Kuchimi, yayin da suka fasa shagona da dama a yayin suke shirin fita daga kauyen”.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar bai dauki wayarsa ba

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige bai amsa kiran wayan da aka masa ba yayin tattara wannan rahoto, jihar Kaduna na cikin jihohin da ke fama da rashin tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An sace shugaban karamar hukuma a Arewa, an kashe dan sandan bayansa

Masu garkuwa da mutane suna addabar mutane da dama a yankunan Najeriya musamman Arewa maso Yamma, yayin da gwamnati ke kara bada tabbacin cewa za su kawo karshen rashin tsaro a fadin kasar.

Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

A wani labarin, Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun yi nasarar kashe kasurgumin ɗan bindigan jeji, wanda ya addabi mutane da dama a jihar.

Bayan sheke ɗan ta'addan, dakarun 'jami'an 'yan sanda sun kwato Babur ɗin da suke amfani da shi a ƙauyen Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa, a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel