'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da halaka wasu masu garkuwa da mutane 3 a jihar Kano
  • An gano cewa sun shiga kauyen Katsinawa da ke karamar hukumar Tudun wada inda suka sace wasu mutum uku
  • Bayan artabun ruwan wuta a dajin Falgore, 'yan sandan sun ceto wasu mutum biyu daga cikin wadanda suka sace

Kano - Jami’an ‘yan sanda a Kano sun yi nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane a kalla uku tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a hannunsu, Vanguard ta ruwaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandanjihar, SP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kashe masu garkuwar ne a wani artabu da ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sifetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane 3 Yayin Da Suke Sallah a Masallaci

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane
'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, SP Haruna ya ce an kubutar da wadanda aka sace ba tare da jin rauni ba, kuma tuni aka mika su ga iyalansu.

A cewarsa, “A ranar Asabar da misalin karfe 01;30 na safe ne aka samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka wa wani kauyen Katsina inda suka sace wani Elisha Aminu a karamar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, suka yi garkuwa da ‘ya’yansa mata guda biyu: Zainab. Elisha, mai shekara 18, Nafisa Elisha mai shekara 16 kuma an kai su gaɓar dajin Falgore.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan samun rahoton kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci tawagar ‘Operation Puff Adder’ jagorancin SP Kabir Aminu, jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Tudun Wada da kuma jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane a karkashin SP Shehu Dahiru domin ceto wadanda aka kashe tare da kamo masu laifin.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

"Kungiyoyin a lokaci guda suka fara aiki tare da taimakon wani rukunin 'yan banga na gida mai suna "Yan Bula". An zagye dajin kuma ‘yan bindigar sun makale, sakamakon haka, an kwashe kimanin sa’o’i 2 ana gwabza artabu da su.
"An halaka uku daga cikin satar mutane, sannan an ceto mutanen biyu ba tare da sun jigata ba . Amma wasu fusatattun mutane kuma sun kona daya daga cikin masu garkuwa da mutane.
“An mik gawawwakin zuwa babban asibitin Tudun Wada inda likita ya tabbatar da mutuwarsu. An sake mika wadanda aka ceto zuwa iyalansu. An tura ƙarin ƙungiyoyin Puff Adder zuwa dajin don ƙarin kame.
“Kwamishanan ‘yan sandan ya jinjinawa jami’an da suka shiga aikin kuma ya yaba da kokarin ’yan banga (‘Yan Bula) bisa goyon baya da taimakon da suke yi."

Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun bankaɗo yunƙurin kai farmaki matatar man fetur ta Dangote, dake Lekki Free Trade Zone cikin jihar Legas.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Talata.

Kamar yadda kakakin ya bayyana, harin ya auku ne a safiyar Litinin, Vanguard ta ruwaito. Ya ce, an daƙile harin da hatsabiban suka yi yunkurin kaiwa ne, yayin kokarin awon gaba da keburan karfen da aka riga aka saka cikin matatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel