Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

  • Mukhtar Aliyu Betara yana samun karbuwa a wajen wadanda za su je majalisa da wadanda suke ofis
  • Wasu sababbin shiga sun tabbatar da cewa kuri’unsu yana wajen ‘dan majalisar na jihar Borno
  • Hon. Betara ya dage duk da ya fito yanki daya daya da zababben mataimakin shugaban Najeriya

Abuja - Wata kungiya da zababbun ‘yan majalisa su ka kafa ta nuna wanda ta ke goyon bayan ya zama shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto, kungiyar ‘New Vision Nigeria’ ta na cikin masu goyon bayan takarar Hon. Mukhtar Aliyu Betara a majalisa.

‘Yan kungiyar ta New Vision Nigeria sun ce dalilinsu na mara baya ga Mukhtar Aliyu Betara shi ne yadda yake haramar taimakawa mutanen Najeriya.

A karshen wani zama da aka yi a garin Gombe, shugaban kungiyar, Ismail Dabo, ya ce su na tare da ‘dan majalisar na Borno ne saboda shi ya fi cancanta.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran da Ake Zargi da Yi wa APC Aiki a 2023 Ya Fito Fili Yana Goyon Bayan Tinubu

Betara ya fi kowa dacewa

‘Dan siyasar da zai wakilci mazabar Toro a majalisar wakilan tarayya ya nuna a jerin masu neman kujerar Femi Gbajabiamila, Betara ne ya fi dacewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto Dabo yana cewa ‘yan kungiyarsu daga jam’iyyu dabam-dabam sun fito ne domin a iya shawo kan matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.

‘Yan Majalisa
Hon. Mukhtar Aliyu Betara a zauren Majalisa Hoto: www.arewareportersng.com
Asali: UGC

‘Dan majalisar mai jiran-gado ya ce ‘Yan Najeriya su na cikin wani irin yanayin wahala, yake cewa dole majalisa tayi abin da za tayi, a taimaka.

"Kafin mu gamsu za mu goyi bayan Mukhtar Betara ya zama sabon shugaban majalisa ta goma, sai da mu ka gayyaci duka masu neman takara
Mun ji irin abubuwan da su ka zo da shi ga majalisa da Kasa. Mun duba tarihinsu, a yanzu haka, Hon. Betara shi ne wanda ya fi kowanensu.

Kara karanta wannan

DCD Ta Gano Makarkashiyar da Ahmad Lawan Suke Shiryawa Kafin Zaben Majalisa

Saboda haka zababbun majalisa mu ka gamsu cewa mu na tare da Mukhtar Betara."

- Ismail Dabo

Betara bai adawa da APC

Ganin rade-radi na yawo cewa yana adawa ga jam’iyya, The Nation ta ce ‘dan majalisar na Biu/Kwayar/Kusar/Bayo/Shani ya karyata zargin.

Bayani ya fito daga ofishin Darektan kamfen, Dickson Tarkighir, aka ji shi yana cewa Betara yana takara ne saboda ya taimaki Gwamnatin Bola Tinubu.

APC ta dakatar da 'ya 'yanta

Idan aka tafi Kudu maso gabas, za a ji labari shugabannin APC sun koyawa wasu jiga-jigan ‘Yan siyasa darasi bayan an binciki abin da suka yi a 2023.

An zargi tsohon Gwamnan Enugu da Sanatan Abia ta Arewa da tsohon shugaban majalisa da wasu da cin amana, don haka jam'iyya ta dakatar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng