Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Bincikar Gwamnatin Ganduje Kan Bashin N241bn

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Bincikar Gwamnatin Ganduje Kan Bashin N241bn

  • Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin bincikar gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje
  • Abba Kabir ya koka kan yadda Ganduje ya bar masa bashin N241 a jihar Kano, inda ya ce hakan ba za ta saɓu ba
  • Sabon gwamnan ya koka kan yadda Ganduje ya sa ƙafa ya tsallake bai jira ya miƙa masa mulki da kansa ba kamar yadda aka saba

Jihar Kano - Gwamna mai jiran gado na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ga sja alwashin bincikar bashin N241 da ya gada daga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Yusuf ya bayyana cewa takardun miƙa mulki da gwamna Ganduje ya bayar ta hannun sakataren gwamnatin jihar mai barin gado, sun yi kaɗan kuma ba su da yawa, cewar rahoton Daily Trust.

Abba Gida-Gida zai binciki Ganduje kan bashin N241bn
Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) Hoto: Newswire.com
Asali: UGC

Ya kuma caccaki Ganduje kan yadda ya sa ƙafa ya tsallake sanannen tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar barin jihar, maimakon ya tsaya da kansa ya miƙa masa ragamar mulkin jihar.

Ya sha alwashin bincikar Ganduje

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayanan miƙa mulkin sun yi mana kaɗan. Bayanai ne ƴan kaɗan. Rahoton kwamitin miƙa mulki shi ma ya yi kaɗan."
"Babu abinda za mu iya yi a matsayin mu na wakilan jiha, ba za mu ƙi karɓar abinda suka bamu ba. Za mu yi duba akai. Inda mu ka gamsu za mu ɗauki mataki, za kuma mu ɗauki mataki a inda ba mu gamsu ba."
"Abin ban takaici ne cewa gwamnatin ta bar mana bashin sama da N241bn. Ta ina za mu samo kuɗin? Kuɗin shigar da su ke magana akai ba wani abin a zo a gani bane. Kuɗin da suka samar ta hanyar hukumar tattara kuɗin shiga ta jiha ba wani abin a zo a gani bane. Za mu duba mu gani. Ban gamsu ba!"

An Yi Wa Sarkin Kano Ihu A Wurin Bikin Rantsar Da Abba Gida Gida

A wani rahoton na daban kuma, wasu fusatattun matasa sun nuna halin rashin ɗa'a a wajen rantsar da sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Matasan sun yi wa sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ihu lokacin da ya iso wajen da ake bikin rantsar da sabon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel