“Abun Tausayi”: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Shiga Daga Ciki

“Abun Tausayi”: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Shiga Daga Ciki

  • Wata mai son sha'anin bikukuwa ta garzaya shafinta na TikTok don nuna yadda wani uba ya sha kuka da hawaye a wajen bikin diyarsa
  • Bidiyon mai taba zuciya ya nuno uban yana kuka yayin da diyarsa ta durkusa a gabansa tana lallashinsa amma ya gaza daina zubar da hawaye
  • Wannan abu da mutumin ya yi ya tsuma zukatan masu amfani da TikTok, wadanda suka garzaya sashin sharhi don nuna sha'awarsu

Wata matashiya wacce ke son tattara bukukuwan aure a mai suna vickkye.alaga a TikTok ta garzaya shafinta don wallafa yadda wani uba ya yi kuka da hawaye a wajen bikin aurensa.

A bidiyon mai tsima zuciya, an gano matashiyar durkushe a gaban mahaifinta yayin da ta rike hannunsa tana lallashinsa.

Uba ya fashe da kuka a bikin diyarsa
“Abun Tausayi”: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Diyarsa Ta Shiga Daga Ciki Hoto: vickkye.alaga
Asali: TikTok

Sauran mutane da ke zaune kewaye da shi sun yi kokarin lallashinsa, amma ya gaza shanye lamarin yayin da ya dunga kuka ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya

Jama'a da suka ga bidiyon a TikTok sun bayyana shi a matsayin mai muhimmanci yayin da wasu suka yi addu'an Allah ya nuna masu irin wannan rana. Yayin da wadanda suka rasa mahaifansu suka ji dama sune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin jama'a a TikTok

@_______yetty ta yi martani:

"Allah, ba don komai ba don Annabi Muhammad ka sa iyayena su ga ranar farin cikina/babban rana☺️"

@kimpemmy ta ce:

"Na roki Allah yasa mahaifina ya iya boye damuwarsa a ranar aurena saboda mutumin nan baya wasa da ni."

@sweetkemzy_16:

"Sai na ci moriyar haihuwana."

@nurse__temmy ta ce:

"Na yi kewarka sosai mahaifina. Allah ya ji kanka da rahama."

@adeola_45270531:

"Mahaifina ina kewarka sosai."

@tahafatie0:

"Mahaifana za su yi tsawon rai don shaida ranar aurena Inshallah."

@fancyberry20:

"Duba ga yadda mahaifin ya yi, shi kadai ya tarbiyantar da yarinyar da duk abun da ya mallaka zai so inama ace mahaifiyar ta tsaya don shaida wannan rana....Ni shaida ce."

Kara karanta wannan

"Yana Iya Zautar Da Mutum": Yadda Matar Aure Ta Ci Amanar Mijinta Na Sunnah, Sam Ba Ta Yi Da Na Sani Ba

Bidiyon sauyawar ma'aurata da suka yi aure tun basu da ko sisi ya yadu

A wani labarin, mun ji cewa wasu ma'aurata sun dauki hankalin jama'a a soshiyal midiya bayan cin karo da bidiyon hotunansu tun basu da komai har zuwa yanzu da Allah ya wadata su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel