“A Dage Auren”: Uba Ya Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Diyarsa Ta Amarce Da Sahibinta

“A Dage Auren”: Uba Ya Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Diyarsa Ta Amarce Da Sahibinta

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta karaya yayin da ta ga mahaifinta yana kuka da hawaye a ranar bikin aurenta
  • A cikin bidiyon da aka wallafa a Instagram, an gano mutumin yana kallon kwayar idanun diyarsa sannan ya fashe da kuka wiwi
  • Da suke martani ga bidiyon mai tsuma zukata, jama'a da dama sun tuna halin da suka shiga da iyayensu a ranar aurensu

Wata matashiya yar Najeriya ta karaya sosai yayin da ta ga mahaifinta ya fashe da kuka wiwi a ranar daurin aurenta.

Bidiyon mai ban tausayi wanda @oluremisan ta wallafa, an gano mahaifin amaryar yana kallon diyar tasa cike da kulawa sai kuma ga hawaye ya gangaro kan kuncinsa.

Uba yana kuka wajen bikin diyarsa
“A Dage Auren”: Uba Ya Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Diyarsa Ta Amarce Da Sahibinta Hoto: @oluremisan
Asali: TikTok

Hakan da ya yi ya baiwa matarsa mamaki inda ta kalle shi cikin kaduwa yayin da take kokarin boye nata kukan.

Kara karanta wannan

“Mai Kama Da Kadangare”: Matashi Ya Koka Bayan Ya Yi Wa Budurwarsa Basaja a Matsayin Wani Daban, Ya Gano Bata Yin Sa

Jama'a sun yi martani

Jama'a sun yi martani mai dadi kan bidiyon yayin da mutane da dama suka tuna yadda iyayensu suka karaya a wajen bikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

@adebisi ta ce:

"Haaa auren nan ba zai yiwu ba fa. Zan fada ma kowa ya tafi gida har sai baba ta gani."

@folakemiakans ta ce:

"Yarinyar nan ta ji dadin soyayyar mahaifi har mahaifiyarta na ta addu'an ta yi ta yi aure ta tafi."

@vickyepelle ta ce:

"Idan mahaifina ya yi kuka, kowa zai tafi gida ne fa. Idan ya yi karfi za mu sake yin auren."

@mojifofo09 ta ce:

"Na san cewa da mahaifina na raye shakka babu zai yi kuka. Allah ya ji kanka mahaifina. Ka tafi amma ba a manta da kai ba."

@godgatmybackstill2020 ta ce:

"Allah kadai ne ya san dalilin da yasa auren uba da ya yake kasancewa, haka mijina da diyata suka dungi kuka a ranar aurenta, a raina na ce ku kuka sani."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Bayan Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara 2, Ma’aurata Sun Gano Su Din Yan’uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

@rnlar5 ta kara da cewar:

"Idan mahaifina ya yi kuka a ranar aurena kawai binsa gida zan yi fa."

Uba ya yi kuka da hawaye yayin da yake sanya wa diyarsa albarka a wajen bikinta

A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewaw ani uba ya fashe da kuka yayin baikon auren diyarsa a cikin wani bidiyo da shafin @ariyike_alaga ya wallafa.

Hawaye na ta zuba daga idanun mutumin har zuwa kan kuncinsa yayin da diyar tasa ta durkusa a gabansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel