“Ta Tura Hotona”: Matashi Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Yi Hira Da Budurwarsa Da Wani Lamba

“Ta Tura Hotona”: Matashi Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Yi Hira Da Budurwarsa Da Wani Lamba

  • Watanni bayan sun fara soyayya, matashi ya lura cewa budurwarsa bata yi masa son gaskiya don haka ya yanke shawarar gwada ta
  • Ya yi wa matashiyar magana da wata lambar waya ta daban inda ya yi basaja kuma ya kadu matuka
  • Ya wallafa yadda ya ta yi ikirarin cewa tsawon shekaru shida bata yi soyayya da kowa ba sannan ta yi masa lakabi da kadangare

Wani dan Najeriya mai suna @Capt_Aliyu, ya ce ya fara dasa ayar tambaya kan soyayya bayan gwajin da ya yi wa budurwarsa don gane ko ba son gaskiya take yi masa ba.

Yayin da yake martani ga wani da ya bukaci mutane su fadi dalilin da yasa suka rabu da tsoffin masoyansu, mutumin ya ba da labarin yadda aka ragargaza masa zuciya a Twitter.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Bayan Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara 2, Ma’aurata Sun Gano Su Din Yan’uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

Hoton budurwa, saurayi da hirar waya
“Ta Tura Hotona”: Matashi Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Yi Hira Da Budurwarsa Da Wani Lamba Hoto: Vandervelden, Shua Taiwo, Panda Security
Asali: Getty Images

Ya bayyana cewa ya gano budurwar na wasa da zuciyarsa ne kawai don haka ya shirya wata dabara don tabbatar da zatonsa.

Mutumin ya zanta da yarinyar ta hanyar amfani da wata lamba ta daban ya kuma kadu da ya ji cewar bata yi Soyayya da kowa ba tsawon shekaru shida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba iya nan abun ya tsaya ba, ta kuma fada masa cewar mutum na karshe da ta yi soyayya da shi yana kama da kadangare kuma cewa wannan dalilin ne yasa ta rabu da shi.

Da ya tambaye ta hoton tsohon saurayinta mai kama da kadangare, sai ta fito da hotonsa.

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama’a sun yi martani

@MilahAhmed ya ce:

“Wannan labarin bai gamsheni ba, kamar akwai kwana-kwana a labarin. Yan mata na kokarin guje na labarai kan tsoffin samarinsu.”

Kara karanta wannan

Matashi Ya Baiwa Mahaifiyarsa Mamaki, Ya Kaita Yawo a Jirgin Sama Don Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta a Bidiyo

@TheoryOfKemi ta ce:

“Na kasa yarda wai na yanzun nan na zubar maka da hawaye.
“Mutane na fuskantar yanayi sosai.”

@HAMBELL4U

“Na ji radadinka ya faru da ni Nima, nagode Allah bata kira ni da kadangare ba amma ta kirani gajere sannan da ta turo mun hoton, sai na ce mata amma wannan bai da aibu Ina kokarin zuzuta kaina amma sai ta ce kada ka damu da hoton gyarawa aka yi ba wanda aka dauka kai tsaye bane.”

Ma'aurata sun gano su yan'uwa ne bayan shekaru 8 da aure harda yara 2

A wani labarin, wata matashiya ta garzaya soshiyal midiya don bayyana wani sirri da suka bankado a rayuwar aurensu.

Ma'auratan da suka shafe shekaru takwas da aure harda yara biyu sun gano cewa suna da alaka ta jini

Asali: Legit.ng

Online view pixel