Gobara Ta Lakume Shaguna 150 a Kasuwar Yan Katako Da Ke Zariya

Gobara Ta Lakume Shaguna 150 a Kasuwar Yan Katako Da Ke Zariya

  • Mumunar gobara ta yi barna a kasuwar yan Katoko da ke yankin Zariya a jihar Kaduna a ranar Laraba
  • Wutan da ya fara ci tun daga tsakar dare har zuwa wayewar gari ya kona shaguna 150 kurmus
  • Hakazalika an yi hasarar dukiya na miliyoyin nairori a gobarar da ta tashi sanadiyar fadowar wayar lantarki

Kaduna - A kalla shaguna 150 ne suka kone kurmus sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar Yan Katako da ke Sabon Gari da ke yankin Zariya, jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewar gobarar da ta fara ci daga karfe 1:00 na tsakar daren jiya ta dungi ci har zuwa rana.

Jama'a sun taru a wajen tashin gobara
Gobara Ta Lakume Shaguna 150 a Kasuwar Yan Katako Da Ke Zariya Hoto: The Cable
Asali: UGC

Yadda gobarar ta fara ci a kasuwar

Hamisu Buhari, babban jami'in tsaron kasuwar, ya ce gobarar ta fara ci ne lokacin da aka dawo da wutar lantarki sannan igiyar wuta ta fada kan rufin daya daga cikin shagunan.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Gobarar ta yadu zuwa sauran shaguna da ke kasuwar."

Buhari ya ci gaba da bayyana cewa duk kokarin da aka yi na jan hankalin hukumomin kwana-kwana a yankin ya ci tura.

Ya ci gaba da cewa:

"Ni da kaina na je ofishin kwana-kwana na Kofar Doka. An sanar da ni cewa motar aikinsu ya lalace. Sai na garzaya sansanin Kongo da ke jami'ar Ahmadu Bello inda aka fada mani cewa an umurcesu da kada su yi aiki a wajen harabar jami'ar.
"A karshe na kira ofishin kwana-kwana na ainahin kasuwar Sabon Gari. Sun bukaci na samar da man fetur wanda na aikata hakan kafin suka amsa mani."

A wata hira da aka yi da shi, shugaban kungiyar masu katako a kasuwar, Alhaji Alin Ashiru, ya ce lamarin ya afku ne a ranar Laraba, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Yan Farin Hula 15 Da Sojoji 2

Ya bayyana cewa shaguna fiye da 150 ne suka kone kurmus kuma cewa dukiyoyi na miliyoyin naira sun lalace.

Ba tartsatin wuta bane ya haddasa gobarar, KEDCO

Da aka tuntube shi, shugaban sashin kula da harkokin KEDCO, Abdul Azeez Abdullahi, ya karyata cewar tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa annobar.

Ya ce rahotanni da aka samu sun nuna cewa gobarar ta fara ne a daya daga cikin shaguna a kasuwar.

Hakazalika, Umar Mohammed, shugaban hukumar Kwana-kwana, Kofar Doka, Zaria ya ce motarsu bata aiki ne saboda hatsarin da ta yi kwanan nan bayan aikin ceto a wajen ajiyar mai na rundunar sojin Najeriya.

Gobara ta tashi a kasuwar Kwara

A wani lamari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa shahararriyar kasuwa ta Oja-Tuntun da ke yankin Baboko a Ilorin, jihar Kwara ta kama gobara inda shaguna shida suka kone.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel