Asiri Ya Tonu: Yan Sanda Sun Gano Masu Shirin Kai Hari Majalisar Dokokin Filato

Asiri Ya Tonu: Yan Sanda Sun Gano Masu Shirin Kai Hari Majalisar Dokokin Filato

  • Rundunar yan sanda ta gano masu shirin kai mummunan hari zauren majalisar dokokin jihar Filato
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce tuni kwamishina ya ɗauƙi matakin kare aukuwar haka
  • Ya kuma gargaɗi duk mai hannu a kulla wannan tuggu ya shiga taitayinsa, idan kuma ya ƙi ji to ba zai ƙi gani ba

Plateau - Rundunar 'yan sanda ta ce ta gano wani boyayyen shirin kai hari zauren majalisar dokokin jihar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Yan sandan Najeriya.
Asiri Ya Tonu: Yan Sanda Sun Gano Masu Shirin Kai Hari Majalisar Dokokin Filato Hoto: Policeng
Asali: UGC

Ya ce manufar masu kulla wannan manaƙisa da makirci shi ne su haddasa rikici da kuma karya doka da oda a zauren majalisar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Masha Allah An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan, Yau Za a Kwaso Da Dama

DSP Alfred ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rundunar 'yan sandan jihar Filato na sanar da ɗaukacin al'umma cewa wasu sahihan bayanan sirri daga majiyoyi masu ƙarfi sun nuna cewa wasu maƙiyan da basu kaunar zaman lafiya na shirin mamaye majalisar dokokin jiha."
"Suna shirin kai farmakin da zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi. Sai dai bayan samun bayanai, kwamishinan yan sandan Filato ya ƙara girke dakaru a kewayen majalisar dokoki domin kare aukuwar haka."
"Saboda haka, hukumar yan sanda na gargaɗin duk mai hannu a shirin kai hari yankin majalisa ko wani wuri a faɗin Filato ya shiga taitayinsa ko kuma ya shirya girban abinda ya shuka a gaban doka idan ya shiga hannu."

Rundunar yan sandan ta kuma roki masu son zaman lafiya a jihar su ci gaba da taimaka wa yan sanda da sahihan bayanai domin su kai ɗauki a kan lokacin da aka neme su.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Alƙalin Babbar Kotun Arewa Rasuwa

Ta kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su gargaɗi 'ya'yansu da sauran waɗanda suke rike da su don gudun kar su shiga harkokin masu son rai, waɗan da zasu yi amfani da su wajen ta da zaune tsaye.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun mako uku da suka shige, jami'an yan sanda suka kwace iko da majalisar dokokin jihar Filato saboda rigimgimun shugabanci.

Yan bindiga sun sace kwamishinar NPC ya ƙasa

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kwamishina a Gwamnatin Buhari

Kwamishinar hukumar ƙidaga ta ƙasa (NPC) a jihar Bayelsa ta faɗa hannun masu garkuwa da mutane ranar Lahadi da yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa mahara sun sace matar ne a jihar Ribas yayin da take hanyar zuwa Patakwal tare da direba da yar aikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel