Masha Allah, An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan

Masha Allah, An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan

  • Ƴan Najeriyan da rikicin ƙasar Sudan ya ritsa da su za su fara baro ƙasar yau Talata 25 ga watan Afirilu
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ita ce ta tsara yadda za a yi jigilar ƴan Najeriyan domin dawowa gida
  • Tuni har motoci ɗauke da ƴan Najeriya suka fara baro Sudan domin tseratar da su daga rikicin

Abuja - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta sanar da fara jigilar kwaso ƴan Najeriya 5,500 da suka maƙale a ƙasar Sudan, yau talata 25 ga watan Afirilun 2023.

A cewar darektan ayyukan musamman na hukumar NEMA, Mr. Onimode Bamidele, tuni har shugaban hukumar ya isa birnin Alkhahira na ƙasar Masar domin daidaita yadda za a kwaso mutanen, cewar rahoton Tribune.

An fara kwaso ƴan Najeriya daga Sudan
Dubunnan mutane ake sa ran kwasowa daga kasar. Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Bamidele ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels Tv a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Daga Dawowa Gida, Tinubu Ya Faɗi Gaskiya Kan Rashin Lafiyarsa, Ya Aike da Saƙo Ga Yan Najeriya

A yayin da ya ke tabbatar da cewa shirye-shirye sun yi nisa sosai kan dawowar su, ya kuma bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzun nan na yi magana da jakandan Najeriya da ke Khartoum, Olaniyan, sannan maganar gaskiya ita ce akwai shirin fara jigilar ranar Talata (yau) da safe, yanzu da na ke magana da ku, shugaban hukumar NEMA, Mustapha Ahmed, yana birnin Alkhahira saboda ta wannan hanyar mu ke so mu yi amfani da ita."
"Akwai wani gari da ake kira da Luxor da kuma wani daban. Don haka ofishin jakandancin Najeriya na Khartoum da shubaban NEMA za su shirya yadda tafiyar za ta wakana cikin tsari."

Ya bayyana cewa ɗalibai da sauran mutane kimanin 5,000 ne ake sa ran kwasowa, amma za a fara kwaso mutum 2,500 zuwa 2,800 ciki har da iyalan ma'aikatan ofishin jakandancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Alƙalin Babbar Kotun Arewa Rasuwa

An fara jigilar daliban

Wani bidiyo da ɓangaren dakarun Rapid Support Forces, ma su yin biyayya ga Janar Hamdan, suka sanya a Twitter, ya nuna wata mota ɗauke da ƴan Najeriya suna shirin baro ƙasar Sudan.

Kamfanin Jirgin Sama Na Air Peace Zai Kwaso 'Yan Najeriya Kyauta

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa kamfanin jirgin sama na Air Peace ya shirya tsaf domin dawo da ƴan Najeriya gida daga ƙasar Sudan.

Shugaban kamfanin, Allen Onyema, shine ya tabbatar da hakan inda ya ce kamfanin sa ya gama shiri domin fara aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel