Alkalin Babbar Kotun Jihar Kwara, Oyinloye, Ya Rasu Yana da Shekara 58

Alkalin Babbar Kotun Jihar Kwara, Oyinloye, Ya Rasu Yana da Shekara 58

  • Rai bakon duniya, Allah ya yi wa Alƙalin babbar Kotun jihar Kwara, mai shari'a Sikiru Adeyinka Oyinloye rasuwa
  • Bayanai sun nuna cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 58 a duniya bayan fama da ciwon wuya tsawon lokaci
  • Mai shari'a Oyinloye, ya shahara a aikinsa saboda ba sani ba sabo kuma ya kama mutane da yawa da hannu a aikata manyan laifuka

Kwara - Mai shari'a Sikiru Adeyinka Oyinloye na babbar Kotun jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Marigayi Alƙalin ya rasu ne ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, 2023 bayan kwashe dogon lokaci yana fama da ciwon da ya shafi wuyansa.

Sikiru Adeyinka.
Alkalin Babbar Kotun Jihar Kwara, Oyinloye, Ya Rasu Yana da Shekara 58 Hoto: thenigerianlawyer
Asali: Twitter

Wata majiya ta bayyana cewa Alƙalin ya taba zuwa ƙasar Indiya neman magani amma ya rasu yana da shekara 58 a duniya yana kan aikinsa.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Arewa Ya Kwaikwayi Buhari, Ya Duƙa Kan Guiwa Yana Neman Talakawa Su Yafe Masa

Marigayi Oyinloye, ɗan asalin kauyen Ijara Isin ne da ke karar hukumar Isin a jihar Kwara. Ya yi aiki a Babalakin & Co. gabanin naɗa shi Alƙalin babbar kotun jihar Kwara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin rasuwarsa, mai shari'a Oyinloye, Alkali ne da ake matuƙar ganin girmansa wanda ya yi kaurin suna wajen 'Ba sani ba sabo' a harkokin shari'arsa kuma yana da kirki.

Ya kama mutane da dama da laifin halasta kuɗin haram bayan hukumar EFCC ta gurfanar da su a gaban Kotu, inda ya umarci a kwace kadarorin da suka yi sama da faɗi da su.

A 2017, Marigayi Alkalin ya maka tarar biliyan N4bn kan jaridar Sahara Reporters da shugabanta, Omoyele Sowore, sakamakon wasu jerin labarai da suka wallafa kan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Haka zalika marigayin ya kama Lakcaran kwalejin fasahar lafiya da ke Offa, Adebisi Ademola, da aikata laifi kana ya ɗaure shi tsawon watanni 6 a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wasu Inyamurai Suka Gudanar da Sallar Idi Ya Ja Hankalin Musulman Najeriya

Ya kama malamin kwalen da hannu a aikata laifin damfarar soyayya a ranar 12 ga watan Maris, 2021, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ɗaliban FGC Yauri Guda Hudu Sun Shaki Iskar Yanci

A wani labarin kuma Bayan Shekaru 2, Ɗaliban FGC Yauri Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga

Ɗalibai mata huɗu daga cikin 11 da suka rage hannun yan bindiga, waɗanda aka sace daga makatantar FGC Yauri, jihar Kebbi sun shaƙi iskar 'yanci.

Rahoto ya nuna cewa iyayensu sun biya maƙudan kuɗin fansa kuma sai da duka shafe kwanaki da yawa suka tattaunawa da shugaban yan bindiga a jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel