‘Tir da Tsiya’: Motar da Ake Kira da Waya Ta Zo Har Inda Ake So Ta Jawo Cece-Kuce a Intanet

‘Tir da Tsiya’: Motar da Ake Kira da Waya Ta Zo Har Inda Ake So Ta Jawo Cece-Kuce a Intanet

  • Wani matashin da ya kira motarsa ta hanyar amfani da wayarsa sannan ta zo ya yadu a kafar sada zumunta ta Instagram
  • A bidiyon, an ga lokacin da matashin ke kiran motar kan ta zo wurinsa ba tare da matuki ko wata matsala ba
  • An kuma ga lokacin da motar ta zo daga wani tazara kana ta tsaya a kusa da matashin, lamarin da ya jawo cece-kuce

Wani matashin da ya mallaki mota mai ban al’ajabi da ke sarrafa kanta ya nuna yadda motar ke aiki ba tare da matsala ba.

A bidiyon da ya yada, matashin ya latsa wasu ‘yan maballai a wayarsa, sai kawai motar ta fara zuwa wurinsa, ta kuma tsaya a inda yace ta tsaya.

Hakazalika, matashin ya yi murmushi tare da bayyana yadda fasahar zamani ke kara daukar hankali a wannan karnin na 21.

Kara karanta wannan

Abun Kallo: Wata Amarya Ta Fusata Ta Hukunta Mijinta Kan Laifi 1, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Yadda wani matashi ya kira motarsa a waya, ta zo da kanta
Lokacin da matashi ke nuna yadda ake amfani da motar | Hoto: @tundednut
Asali: TikTok

A cewarsa, a 2023 motoci za su iya zuwa ga masu su wanda kuma hakan abu ne mai daukar hankali da ke nuna kwarewa wajen fikirai fasihai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yawan jama’a a kafar sada zumunta da suka bidiyon sun ce, za su so mallakar irin wannan mota, sun roki Allah ya taba su da talauci.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@anniesxclusive:

“Allah ya raba ni da iyalai na dandana talauci amin.”

@hairmonybeautyclinic:

“Duk wannan bashi da wani tasiri a kiyama.”

@johnbull3140:

“Allah ya raba ni da talauci a rayuwata.”

@umalistifanus:

“Kai Allah ya raba ni da talauci.”

@nasty_perry_:

“@teslamotors za su mamaye duniya nan kusa.”

@offeciallauretta:

"A rayuwar nan kawai ka tara kudi.”

@karaokewithknaci:

“Bari na samu meye zan ci tukuna.”

@ifeanyigodson:

“Ba zan kara zuwa ga mota ba har abada.”

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Ce Saurayi Da Ya Mallaki Miliyan N2 a Asusunsa Ne Kadai Zai Iya Soyayya Da Ita, Bidiyon Ya Yadu

Rikici ya barke tsakanin mata da miji bayan gano zai kara aure

A wani labarin kuma, wani miji da matarsa sun kaure da rikici bayan da suka gama kudi domin amfani dasu nan gaba, amma suka ci amanar juna.

Wannan lamarin ya zo da tsaiko, inda mijin ya lallaba ya cire wasu kudade tare da buya don kara aure da kudaden da kusan na matarsa ne.

Wani ya shiga tsakani, an gaza samun mafita tsakanin mata da miji domin kowa ya ce kudin nasa ne ba dan uwansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel