“Duk Saurayin Da Ke Son Soyayya Da Ni Dole Ya Mallaki N2m”: Matashiya Mai N3k a Asusu Ta Bayyana

“Duk Saurayin Da Ke Son Soyayya Da Ni Dole Ya Mallaki N2m”: Matashiya Mai N3k a Asusu Ta Bayyana

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ya cewa koda dai bata ra’ayin kudi, dole duk mutumin da zai yi soyayya da ita ya kasance yana da miliyan N2
  • Mutumin da ya nemi ta fadi ra’ayinta ya fashe da dariya da ya ji cewa N3k me kacal da ita a asusunta
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon matashiyar sun ce ta tsawwala da yawa alhalin asusunta a bushe yake kandas

A wani bidiyo da @rebelanon ya saki, wata matashiya yar Najeriya ta magantu game da adadin kudin da dole sai saurayi ya mallaka kafin ya yi soyayya da ita

Matashiyar ya ce dole asusun mutumin ya kasance dauke da miliyan 2 koda dai ba kudi take bi ba. Da aka tambaye ta nawa ne a asusun bankinta ta amsa da, “N3k”.

Kara karanta wannan

“A’a, Ba Zan Iya Ba”: Matashi Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ba Zai Iya Auren Macen Da Ke Karban N5m Duk Wata Ba, Bidiyon Ya Yadu

Matashiya tana hira da wani saurayi
“Duk Saurayin Da Ke Son Soyayya Da Ni Dole Ya Mallaki N2m”: Matashiya Mai N3k a Asusu Ta Bayyana Hoto: @rebelanon
Asali: TikTok

Sharadin da matashiya ya gindaya na yin soyayya ya haddasa cece-kuce

Matashin (@rebelanon) wanda ya magantu da ita a kamara ya kasa daina dariya. Maza da dama sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra’ayinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da wasu suka ce ita diyar kirki ce tunda ta fadi gaskiya, wasu na ganin sharadinta na soyayya da mutum ba mai yiwuwa bane.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon ya tattara martani fiye da 800 da ‘likes’ fiye da 16,000.

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin:

Collinsmuna ta ce:

“N2m bai baci ba, duk da haka diyar kirki ce.”
“N2m ya yi kadan ga magidanci amma wannan 3k din bai kai chajin cire miliyan 2 ba.”

StarBoy dey.4.U ya ce:

“Kuna dai nan kuna ta cewa 2m ya yi kadan wasu daga cikinku basu da N500k a asusu.”

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

FERRY ya ce:

“N2m a ina nawa me albashina 300k bayan cire kudaden abubu 50k nake ragewa da shi.”

Ba zan iya soyayya da wacce ke karbar N5m a matsayin albashi ba, matashi ya magantu

A wani labari makamancin wannan, wani matashin saurayi ya bayyana cewa ba zai yarda ya auri duk macen da ke karbar naira miliyan biyar a matsayin albashin wata ba.

A cewarsa, idan har ya yarda ya aure ta toh shakka babu sai ta ci kashi a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel