“Allah Na Halitta”: Matashi Ya Tunkari Budurwa a Gaban Mahaifiyarta, Ya Mika Mata Wasikar Soyayya

“Allah Na Halitta”: Matashi Ya Tunkari Budurwa a Gaban Mahaifiyarta, Ya Mika Mata Wasikar Soyayya

  • Wata kyakkyawar budurwa ta cika da mamaki lokacin da wani matashin saurayi ya tunkareta a kantin siyayya a Abuja
  • Matashiyar ta karanta wasikar da ya bata sannan ta gaza daina murmushi saboda dadadan kalaman da ya yi a kanta
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun bayyana cewa matashiyan na da kyau kuma za su so mallakar lambarta

Wani matashi dan Najeriya, @mjrplusofficial, wanda ke yin bidiyoyi game da baiwa mutanen da baka sani ba wasikun soyatta ya yi wani da ya kunshi matashiya da mahaifiyarta a wani kanti.

Duk da mahaifiyar matashiyar na kusa, mutumin ya mika hannunsa zuwa wajen yarinyar kunshe da wasikar a tafin hannusa. Matahiyar ta kagu.

Matashiyar budurwa a kantin siyayya
“Allah Na Halitta”: Matashi Ya Tunkari Budurwa a Gaban Mahaifiyarta, Ya Mika Mata Wasikar Soyayya Hoto: @mjrplusofficial
Asali: TikTok

Matashi ya tunkari kyakkyawar yarinya

Bayan ta warware takardar sannan ta karanta, matashiyar ta fashe da dariya. Wasikar na cewa:

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Afrilu: Buhari Ya Fadi Dalilin Da Yasa Baya Fargabar Mika Mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lauyoyi na karantar shari'a. Likitoci na karantar magunguna amma idan za a bani dma, ke zan karanta."

Matashiyar ta kankame mahaifiyarta cikin dariya yayin da ta cika da mamakin yadda ya tsara wasikar soyayyar. Mutumin ya bayyana cewar matashiyar na da kyau.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Cute Mammie ta ce:

"Ya kamata a fadi gaskiya, tana da kyau."

Kennycash ya ce:

"Dan Allah ku dunga saka sunan shafinsu wasu lokutan...ta yaya zan gano babita yanzu."

Taiyes 1994 ya ce:

"Ina ma ace na santa sani na gani ga ki."

aremuu o4 ya ce:

"Idan da jikinta darasi ne za ka karance shi tana da kyau dari bisa dari."

teebago247 ta ce:

"Uwa da ya masu kyau har zuciya Allah ya albarkace su."

Legendary Bolt 001 ya ce:

"Maza yarinyar nan na da kyau."

Kara karanta wannan

Yadda Saurayi Ya Sheke Budurwarsa a Kaduna, Ya Ce Ya Kashe Mata Kudi Masu Yawan Gaske Amma Ta Yi Kokarin Rabuwa Da Shi

He ya ce:

"Idanunka na rudarka dan uwa. Kana gani da kyau kuwa."

A kullun sai na yi wa mijina wankin kayansa sannan na gyara gida, Matashiyar lauya

A wani labari na daban, wata matashiyar lauya yar Najeriya ta bayyana yadda take kula da gidan aurenta da kuma mijinta a lokaci guda ba tare da gajiyawa ba.

Matashiyar matar ta ce duk kwanan duniya tana wanke kayan mijinta da kanta sannan ta gyare gidansu koina ya yi tsaf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel