“Na Kashe Mata Kudi Da Yawa”: Matashin Da Ya Kashe Budurwarsa a Saboda Ta Yi Kokarin Rabuwa Da Shi Ya Magantu

“Na Kashe Mata Kudi Da Yawa”: Matashin Da Ya Kashe Budurwarsa a Saboda Ta Yi Kokarin Rabuwa Da Shi Ya Magantu

  • Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kama wani matashi da ya sheke budurwarsa
  • Mai laifin ya ce ya kashewa budurwar tasa makudan kudi amma sai ta yi kokarin rabuwa da shi saboda wani daban
  • Jami'an yan sandan sun kwaci matashin daga hannun fusatattun matasa yayin da suke gab da halaka shi

Kaduna - Jami'an rundunar yan sandan jihar Kaduna sun kama wani mutum wanda ake zargi da kashe budurwarsa saboda ta yi kokarin rabuwa da shi.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya bayyana a ranar Juma'a cewa an kama mai laifin, wanda ya kashe budurwarsa yayin da fusatattun matasa suka yi yunkurin kashe shi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
“Na Kashe Mata Kudi Da Yawa”: Matashin Da Ya Kashe Budurwarsa a Saboda Ta Yi Kokarin Rabuwa Da Shi Ya Magantu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda al'amarin ya faru, rundunar yan sanda

Jaridar ta nakalto DSP Jalige yana cewa:

Kara karanta wannan

“Ya Siya Gidaje, Motoci, Ya Tura Mutane Umrah”: Mai POS Ya Kashe Miliyan N280 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A ranar 14 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:00 na dare, mun samu wani kira mai cike da damuwa cewa akwai wasu da suka yi kokarin kisan kai a shataletalen NEPA sannan cewa wasu sun so kashe wani mai laifi.
"An tura jami'ai zuwa wajen, inda suka hadu da mai laifin kwance babu inda yake kuma jama'a suka kewaye shi.
"Bayanan da aka tattara ya nuna cewa wanda ake zargin mai suna Kenneth wanda ba a san sunansa ba, ya farmaki budurwarsa mai suna Ebenezer Agada mai shekaru 27.
"Tana zaune a makarantar sakandare na Command da ke Sokoto Road. Ya farmaketa da adda sannan ya ji mata raunuka a fuska, kafada da hannaye.
"A cikin farmakar nata ne, ya lalata mata hannu daya gaba daya, yana mai zargin cewa ya kashe kudi da yawa a kanta sannan ta yi kokarin rabuwa da shi saboda wani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Za Tayi Wa Ma’aikata Karin Albashi a Afrilu Saboda Cire Tallafin Fetur

"An kwashi wacce ake zargin zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko don samun kulawar likita, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarta.
"An dauki gawar nata zuwa wajen ajiyar gawa na asibitin domin yin gwaji, yayin da ake gudanar da bincike a yanzu haka."

Ina yi wa mijina wanki a kullun sannan na gyara gida, matashiyar lauya ta magantu

A wani labarin kuma, wata matashiyar lauya ta garzaya soshiyal midiya don bayyana yadda take gudanar da harkoki a cikin gidan aurenta.

Matashiyar lauyar ta ce tana yi wa mijinta wankin kayansa duk kwanan duniya sannan ta yi gyaran gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel