“Ina Wanke Kayan Mijina Duk Kwanan Duniya”: Matashiyar Lauya Ta Magantu, Ta Fadi Dalilanta

“Ina Wanke Kayan Mijina Duk Kwanan Duniya”: Matashiyar Lauya Ta Magantu, Ta Fadi Dalilanta

  • Wata matashiyar lauya ta garzaya soshiyal midiya inda ta magantu kan abubuwan da take yi a gidan aurenta
  • Ta ce tana wanke kayan mijinta duk kwanan duniya, tana gyara gida sannan ta ciyar da shi abinci yayin da take rike da kwanon wanke hannunsa
  • Rubutun nata ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da dama suka jinjina mata

Wata lauyar Najeriya mai suna Princess Jemaimah ta bayyana cewa tana wanke kayan mijinta duk kwanan duniya.

Princess ta bayyana hakan ne a Facebook yayin da take jero wasu rawar gani da ayyukan da take yi a gidan aurenta.

Matashiyar lauya da wallafarta na Facebook
“Ina Wanke Kayan Mijina Duk Kwanan Duniya”: Matashiyar Lauya Ta Magantu, Ta Fadi Dalilanta Hoto: Princess Jemaimah
Asali: Facebook

Ta kara da cewar tana gabatar masa da abinci sannan ta rike masa kwano don ya wanke hanayyensa sannan ta kuma gyara gidan a kullun kwanan duniya.

A cewar Princess, yin wadannan ayyukan gaba daya bai rageta da komai ba kuma ta bayyana cewa abun tinkaho ne ma ka dunga kula da wani ba tare da gajiyawa ba.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru a Amurka, Matashiya Ta Dawo Najeriya Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan Uwanta Ya Gina Mata, Ta Sharbi Kuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa wasu lokutan su kan yi ayyukan tare, tana mai cewa mijinta ya fi zuwa mata aike fiye da yadda take zuwa ma kanta.

Lauyar ta bayyana cewa gida mai cike da farin ciki wuri ne na kaunar juna ba tare da iyaka ba, sadaukarwa da kuma yafiya.

Jama'a sun yi martani

Prince Denzel ya ce:

"Ya yi kyau malama, amma a kowani aure, ka gane abun da zai yi maka aiki sannan ka rike shi... Tsarin Mista A ba lallai bane ya yi wa Mista B aiki ba domin dukkaninsu suna da manufofi daban-daban don samun sakamako iri guda wanda shine gida mai farin ciki."

Amarachi Jonah Uduma ta ce:

"Hakan ya yi kyau tunda ya yi maki aiki a gidanki kuma abu mai kyau ne sanin cewa yana taka rawar ganinsa babu wanda aka matsawa.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Yadda kiriniyar tagwaye ya sanya uwa kuka, ta goye su a lokacin daya

"Za mu kasance da injin wankinmu da komai ko fasahar da zai saukaka mana a rayuwa."
"Amin."

Eke Sax Johnson ya ce:

"Momi ba mu fahimci na karshen nan ba, dan Allah ki yi karin haske."

A wani labarin, wasu ma'aurata da ke unguwar mallam shehu sun burge zukata da dama da irin soyayyar da suke nunawa junansu duk da rashin kasancewarsu masu arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel