Buhari Ya Kammala Umrah, Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki 8 a Kasar Saudiyya

Buhari Ya Kammala Umrah, Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki 8 a Kasar Saudiyya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan ziyarar Umrah na tsawon kwanaki takwas da ya yi a kasar Saudiyya mai tsarki
  • Shugaban ya tarbi manyan jiga-jigan ‘yan Najeriya a Saudiyya a lokacin da ya hada taron buda baki na azumin Ramadana a ziyarar
  • Ba wnanan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zuwa Saudiyya domin ziyarar ibada ba

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a Abuja bayan shafe kwanaki takwas a tafiyarsa ta kasar Saudiyya ibadan Umrah, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya baro kasar Saudiyya ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah a ranar Laraba 19 Afirilu, 2023.

A cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya, gwamnatin Saudiyya, sarakunan gargajiya da malaman addini daga Najeriya da manyan jami’an jakadancin Najeriya a Saudiyya ne suka yiwa Buhari bankwana a Jeddah.

Kara karanta wannan

Sunayen Jerin Sarakuna, Shehunan da Suka Yi Buda Baki da Shugaban kasa a Makkah

Buhari ya dawo daga Makkah
Shugaban kasa Muhammadu yana sauka daga jirgi | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Buhari ya yi Umrah a ranar Alhamis din da ta gabata

A ranar Alhamis din da ta gabata, Buhari ya yi Umrah a Saudiyya zagaye da jami’an tsaro a lokacin da isa masallacin Makkah mai alfarma daga birnin Madina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, Buhari ya kai ziyara wasu wuraren tarihi masu daraja a Madina a ranar Talata da Laraba kafin gangarawarsa zuwa Makka don ibadar Umrah, rahoton The Nation.

A bangare guda, a can birnin Makkah, Buhari ya karbi bakuncin manyan jiga-jigan Najeriya da suka hadu a can don yin buda bakin azumin Ramadana.

Musulami daga bangarori daban-daban na duniya na zuwa ziyarar aikin Hajji ko Umrah a kasar Saudiyya a lokuta daban-daba.

Duk da wannan, ba karon nan ne na farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kai ziyara kasa mai tsarki ba.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban EFCC, Gwamnoni, Buratai Suka Fadawa Buhari da Aka Hadu a Saudi

Ba lallai a yi sallar Idi ranar Juma’a ba, inji masana

A wani labarin kuma, rahoto ya bayyana cewa, ba lallai a yi sallar azumin Ramadana a ranar Juma’a mai zuwa ba duba da yanayi da kuma yadda watan Ramadana ya zo bana.

Wannan na zuwa ne daga wani hasashe da binciken da masana suka yi a daukar Larabawa, inda suka bayyana abin da suka hango na yanayin ganin watan Shawwal.

A cewarsu, a yankin Larabawa ba a za a ga wata ba a ranar Alhamis, don haka zai iya yiwuwa a tashi da azumi a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel